Rikicin kabila: 'Karancin abinci ya mamaye jihar Taraba

Rikicin kabila: 'Karancin abinci ya mamaye jihar Taraba

Rikici a tsakanin kabilar Tiv da Jukun da ya ki ci ya ki cinyewa ka iya haddasa annobar karancin abinci a jihar Taraba dake Arewa maso Gabashin Najeriya.

Rikicin da ya kunno kai tsawon watanni uku da suka gabat ya ritsa da dubunnan manoma a yankunan Wukari, Donga, da kuma wasu sassa na yankunan karamar hukumae Takum kamar yadda manema labarai na jaridar Daily Trust suka bayar da shaida.

Da yawa daga cikin manoman kauyukan Wukari, Donga da kuma garin Takum sun kauracewa gonakin su yayin da wasu dama suka tsallaka jihar Benuwai dake makwabtaka da su domin neman mafaka.

Bincike ya tabbatar da cewa, yankunan da rikicin ya hana ruwa gudu sun kasance kan sahu na gaba ta fuskar samar da amfanin noma yayin da suke tanadin kimanin kaso 80 cikin dari na doya, masara, gyada da kuma shinkafa dake amfanar al'ummar Kudancin jihar Taraba.

KARANTA KUMA: Adadin al'ummar Najeriya ya kai 190m - NPC

A cikin makon da ya gabata, rayukan manoma daga bangarorin kabilun biyu sun salwanta. Wannan mummunann lamari ya sanya manoma da dama suka kaurace wa gonakin su.

Shugaban karamar hukumar Wukari, Adi Daniel, ya shaidawa manema labarai cewa manoma da dama sun rasa rayukan su da a halin yanzu ya zamto babban hatsari kai ziyara gona muddin zaman duniya bai ishe mutum ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel