Elisha Abbo: Hadimar Buhari tace lallai sai dai a tura sanatan gidan yari

Elisha Abbo: Hadimar Buhari tace lallai sai dai a tura sanatan gidan yari

- Yan Najeriya na ta fadin ra’ayinsu akan irin hukuncin da ya kamata ayi wa Sanata Elisha Abbo, wanda aka zarga da cin zarafin wata mata

- Daya daga cikin hukuncin da Lauretta Onochie, hadimar Shugaban kasa a shafukan zumunta, ta bayar da shawara shine tura sa gidan wakafi

- Onochie ta bayyana cewa yan Najeriya ba za su ji dadi ba, idan har aka yi jinkiri ko rashin yin abunda ya kamata a shari’ar Sanata Abbo

Hadimar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafukan zumunta, Lauretta Omochie, ta nuna farin ciki akan batun cewa an gurfanar da Sanata Elisha Abbo, wanda aka zarga da cin zarafin wata mata a Abuja a gaban kotu a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli.

Onochie ta shawarci kotu da tayi nazarin hujjar da aka gabatar akan Sanata Abbo sannan ta yanke masa zaman gidan yarin da ya cancanta.

Hadimar Shugaban kasar ta bayyana cewa yan Najeriya ba za su ji dadi ba, idan ba a yi adalci ba ko kuma idan aka bashi tarin jin dadi yayinda yake zaman gidan wakafi.

KU KARANTA KUMA: Na yi danasanin rashin mika mulki ga dan takarar da na so – Tsohon gwamna Yari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Hukumar yan sandan Najeriya hallaro da Sanata Elisha Abbo kotun Majistare dake unguwar Zuba, Abuja domin gurfanar da shi kan laifin cin zarafi.

Jaridar Punch ta bada rahoto ranar Lahadi cewa hukumar yan sanda za ta gurfanar da Sanatan a wannan mako bayan abubuwan da suka faru a makon da ya gabata.

Hakazalika kwamishanan yan sandan birnin tarayya, Bala Ciroma, ya tabbatar da labarin cewa an kai Sanata Elisha Abbo kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel