Za mu gina asibitoci masu cin gado 400 a sabbin masarautu 4 na Kano - Ganduje

Za mu gina asibitoci masu cin gado 400 a sabbin masarautu 4 na Kano - Ganduje

Gwamnatin jihar Kano za ta habaka gine-ginen wasu manyan asibitoci a sabbin masarautu hudu da ta kafa inda za ta mayar da su masu cin gado 400 kamar yadda gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana.

Furucin gwamna Ganduje ya zo ne a ranar Asabar 6 ga watan Yuli yayin da yake gabatar da gaisuwar ta'aziyya a fadar Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar, biyo bayan rasuwar dan sa, Alhaji Aliyu Tafida.

Gwamna Ganduje cikin yakini da kuma bayar da tabbaci ya ce habaka gine-ginen asibitocin a masarautun hudu zai wadatar dasu dukkanin kayayyakin bukata wajen kula da lafiyar al'umma na fadar su.

A cewar sa, wannan yunkuri na habaka asibitocin a masarautun Rano, Bichi, Gaya da kuma Karaya zai rage yawan dogaro ga sauran asibitoci da ke cikin tantangwaryar birnin Kanon Dabo.

Ganduje wanda ake yiwa lakabi da Khadimul Islama ya jaddada cewa, samar da sauki na rayuwa ga al'umma na daya daga cikin muhimman dalilai na kafa sabbin masarautu hudu tare da yaduwar ci gaba a dukkanin garin Kano da kewaye.

KARANTA KUMA: Hatsari: Rayuka 2 sun salwanta, mutane 9 sun jikkata a hanyar Ibadan zuwa Legas

Ya kara da cewa, duba da bukatar dawwamar ci gaba a fadin jihar Kano, ya sanya gwamnatin sa ta jajirce wajen tabbatar da kyakkyawar alaka da kuma dangantaka da masarautun gargajiya wajen bunkasa harkokin tsaro, kiwon lafiya, ilimi, zamantakewa da kuma hadin kai a tsakanin al'umma.

Cikin na sa jawaban, Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar, ya yabawa dattako da kuma hangen nesan gwamna Ganduje musamman wajen kawo karshen nakasu da kuma koma bayan da sabbin masarautun Kano ke fuskanta a yanzu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel