Sojoji sun samu gagarumar nasara akan yan bindiga a jahar Zamfara

Sojoji sun samu gagarumar nasara akan yan bindiga a jahar Zamfara

Dakarun Sojojin dake tabbatar da tsaro a jahar Zamfara a karkashin aikin Operation sharan daji sun halaka wasu gungun yan bindiga a dajin Dumburum dake jahar, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar, Laftanar Abayomi Oni-Orisan ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 5 ga watan Yuli, inda yace dakarun Sojan sama sun saukan da ruwan bama bamai akan wasu sanannun sansanonin yan bindiga a dajin Dumburum.

KU KARANTA: Nasara a kotun koli: Buhari ya taya gwamnan jahar Osun murna

“A dalilin haka yan bindiga da dama suka mutu, amma yayin da Sojojin kasa suka zagaye yankin suna sintiri sun ci karo da wasu gungun yan bindiga 10 da suke kokarin tserewa, suma anan suka gamu da ajalinsu a hannun Sojojin.

“Haka zalika Sojojin daga bisani sun kama wasu yan bindigan guda hudu, tare da kama babura guda 2, da kuma shanu 43 da suka sata daga hannun mutanen kauye.” Inji kaakakin rundunar, Laftanar Abayomi.

A wani labari kuma, Sojoji sun samu nasarar halaka wasu yan bindiga da adadinsu ya kai 20 a yayin da suke gab da kaddamar da hari a wani kauyen jahar Katsina da ake kira Munhaye.

Sai dai samun labarin shirin kai harin nasa keda wuya, rundunar Sojan sama ta aika jirgin yakinta guda daya, wanda ya bude musu wuta, har sai daya kashe yan bindiga guda 20 daga cikin 30 dake tattare a wajen.

Daga karshe kaakakin yace rundunarsu ta samu irin wannan nasara ma a jahar Zamfara inda ta kashe yan bindiga da dama a wani dauki ba dadi da suka kwasa da juna a kauyen Bawan Daji dake cikin karamar hukumar Anka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel