'Yan sanda za suyi sulhu tsakanin 'yan bindiga da 'yan kungiyar 'Sa Kai' a Zamfara

'Yan sanda za suyi sulhu tsakanin 'yan bindiga da 'yan kungiyar 'Sa Kai' a Zamfara

Rundunar 'Yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara, a ranar Alhamis ta ce za tayi sulhu tsakanin wasu da ake zargin 'yan bindiga ne da 'yan kungiyar tsaro na sa kai da aka sani da vigilante.

A dalilin hakan jami'an tsaron na sa kai suka saki 'yan bindiga Fulani 25 da ke tsare a hannunsu a watan Afrilun domin wanzar da zaman lafiya a jihar ta Zamfara.

Mai magana da yawun 'yan sanda, Mohammed Shehu ya ce an saki 'yan bindigan ne sakamakon sulhun da 'yan sanda ke yi tsakanin 'yan bindigan da 'yan kungiyar tsaron na vigilante.

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: Tsohon ministan PDP da dan sa sun karbi katin zama 'yan APC

A cewar 'yan sandan, "Yau 4 ga watan Yulin 2019, Kwamishinan 'Yan sanda, Usman Nagogo ya yi nasarar karbo Fulani 25 da aka tsare da su tun ranar 9 ga watan Afrilun 2019 a hannun 'Yansakai a masarautar Dansadau da ke karamar hukumar Maru na jihar Zamfara.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya kara da cewa wadanda aka saki sun hada da mata, maza da yara kanana.

Yayin da ya ke karbar wadanda ake sako, Kwamishinan 'Yan sandan ya yabawa kungiyar tsaron na sa kai saboda cika alkawarri da su kayi na sakin wadanda suke tsare da su. Ya bukaci kungiyoyin biyu su zauna lafiya.

Daga bisani an tafi da wadanda aka sako zuwa gidan gwamnati.

Sarkin Dansadau ya mika godiyarsa ga Rundunar 'Yan sanda da gwamnatin Jihar saboda daukan matakin gaggawa da su kayi na kawo zaman lafiya a jihar.

A jawabinsa, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya mika godiyarsa ga rundunar 'yan sanda saboda aikin da ya keyi na kawo zaman lafiya a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel