Wata Mata ta yi ma mijinta dukan tsiya har sai daya fadi matacce a Kano

Wata Mata ta yi ma mijinta dukan tsiya har sai daya fadi matacce a Kano

Ke duniya ina zaki damu ne? wannan irin rayuwa da muke ciki abar tsoro ce, sai kaga masoya suna soyayyarsu rumi rumi kamar da gaske, amma sai bayan biki sai miji ya zama ajalin matarsa, ko kuma ita matar ta zama ajalinsa.

Wannan shine kwatankwacin abin daya faru a unguwar Darmnawa bayan gandun Sarki a cikin garin Kano, inda wani magidanci ya gamu da ajalinsa a hannun matarsa sakamakon cacar baki daya kaure a tsakaninsu.

KU KARANTA: NAFDAC ta kama sundukai 21 makare da rubabbun kifi da aka shigo dasu Najeriya

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Ahmad Deedat ne ya bayyana haka a shafinsa, inda yace rikici ne ya fara kaurewa tsakanin matar da makwabtansu akan fadan yaransu, ana cikin wannan rikici ne sai mijin ya dawo ya tarar dasu.

Sai dai ba tare da wata wata ba mijin ya kora yaransa gida tare da matar tasa, sa’annan ya baiwa makwabtan hakuri. Ashe wannan mataki daya dauka bai yi ma matar tasa dadi ba, don haka ta shirya masa mugunta.

Shigan gida keda wuya sai ta shammaceshi da wani katon katako, ta dinga maka mishi, ta yi ta maka masa babu kakkautawa har sai daya yanke jiki ya fadi, daga nan yace ga garinku nan.

Amma zuwa lokacin tattara wannan rahoto babu tabbacin ko Yansanda sun kama wannan muguwar mata.

A wani labarin kuma, har yanzu tana kasa tana dabo a rikicin daya kaure tsakanin wasu sabbin ma’aurata a jahar Kano, inda Amarya mai suna Hanan ta yi kokarin halaka mijinta ta hanyar caka masa wuka, har sai da hanjin cikinsa suka fito.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel