Majalisar dokokin jihar Kaduna ta tabbatar da kwamishinoni 11
Majalisar dokokin jihar Kaduna a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli ta tabbatar da mutane 11 wadanda gwamna Nasir El-Rufai ya gabatar a matsayin kwamishinoni a jihar.
Daga cikin wadanda aka tabbatar akwai kakakin gwamnan, Samuel Aruwan a matsayin kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida.
Yan majalisar sun fara tabbatar da Mohammed Bashir Saidu wanda ya kasance tsohon kwamishinan kudi da shugaban ma’aikata ga gwamnan jihar a gwamnatin da ya gabata.
Ba da bata lokaci ba Yan majalisar suka bukaci yayi biyayya ya tafi saboda yayi ma jihar hidima a mukamai da dama a cewar kakakin majalisa Aminu Shagali.
Mutum na biyu da aka tabbatar shine Jafaru Ibrahim Sani daga karamar hukumar Kubau wanda ya kasance tsohon kwamishinan ilimin na jihar a gwamnatin da ya gabata. Shi ma yayi biyayya ba tare da tambayoyi ba.
An tantance Hafsat Mohammed Baba a matsayin kwamishinar ma’aikatar ayyuka da cigaba inda majalisar ta bukace ta da tayi biyayya ta tafi, kamar yanda aka bukaci Samuel Aruwan wanda yayi bauta a matsayin babban hadimin gwamna kan kafofin yada labarai da sadarwa wanda a halin yanzu an tabbatar da shi a matsayin kwamishinan tsaron gida da harkokin gida.
KU KARANTA KUMA: Ana shirin kai wadanda suka daura aure a Facebook kotu a Kano
Sauran kwamishinonin da aka tabbatar sun hada da Mohammed Shehu Usman Makarfi wanda ya kasance sakatare na dindindin a ma’aikatar kiwon lafiya a matsayin kwamishinan ilimi.
Idris Samaila Nyan na ma’aikatar kasuwanci, kirkire-kirkiren fasaha da Ibrahim Garba Hussaini a Ma’aikatar muhalli da albakatu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng