Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da wani babban likitin asibitin Malam Aminu Kano tare da 'yan uwansa guda biyu
- Yanzu muke samun rahoton cewa wasu masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da wani babban likitan Asibitin Malam Aminu Kano
- Barayin sun sace likitan ne akan babbar hanyar Lokoja zuwa Okene shi da kannansa guda biyu
- Wani dan uwansu ya bayyana cewa likitan da kannan nasa suna kan hanyarsu ta zuwa garin Okene ne domin yin addu'ar arba'in ga mahaifiyarsu da ta rasu
Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a san ko su waye ba, sun sace wani likitan Asibitin Malam Aminu Kano, mai suna Dr. Bashir Zubayr, akan babbar hanyar Lokoja zuwa Okene.
An sace Bashir tare da da wasu kannansa guda biyu a kusa da Irepeni kilomita 20 zuwa garin Lokoja ranar Laraba da rana.
Wani dan uwansu ya bayyana cewa likitan da 'yan uwan nasa suna kan hanyarsu ta zuwa Okene domin, yin adduar araba'in ga mahaifiyarsu da ta rasu.
KU KARANTA: Tirkashi: Hukuncin shekara 10 ne kan Sanata Abbo wanda ya ci zarafin mace - CSP Dolapo Badmus
Daga baya an bayyana cewa an gano motar Dr. Zubayr a Irepeni da kofofinta a bude.
A wannan makon ne rundunar 'yan sanda karkashin jagorancin Abba Kyari ta ceto rayuwar Hakimin Daura, wanda aka sace shi watanni biyu da suka gabata.
Matsalar garkuwa da mutane taki ci taki cinyewa dai a kasar nan, duk kuwa da irin kokarin da jami'an tsaro suke yi na ganin sun kawo karshen lamarin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng