Dukan mata: Atiku Abubakar ya kwance ma Sanata Ishaku zani a Kasuwa

Dukan mata: Atiku Abubakar ya kwance ma Sanata Ishaku zani a Kasuwa

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kwance ma Sanata Elisha Ishaku Abbo Cliff zani a kasuwa.

Legit.ng ta ruwaito an dauki hoton bidiyon Sanata Abbo Cliff yana sharara ma wata mata mai shayarwa mari a wani shago dake babban birnin tarayya Abuja, wanda hakan ya harzuka yan Najeriya, kuma ya janyo cece kuce a shafukan sadarwa.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kwalejin kimiyyar lafiya

Dukan mata: Atiku Abubakar ya kwance ma Sanata Ishaku zani a Kasuwa
Dukan mata: Atiku Abubakar ya kwance ma Sanata Ishaku zani a Kasuwa
Asali: Facebook

Atiku ya bayyana bacin ransa game da wannan lamari a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Facebook, inda yace ya san Sanata Elisha farin sani, kuma bai ji dadin ganin bidiyon ba, amma ya bayyana cewa dolene a bari doka ta yi halinta.

“Na kallo bidiyon dukan da Sanata Elisha Abbo yayi ma wata mata, ban ji dadin bidiyon ba, kuma bai kamata a lamunci irin haka ba, na san Sanatan sosai, amma doka a bayyana take, kuma dole ne shuwagabanni su yi jagoranci abin koyi.

“Don haka ina bashi shawara daya nemi gafarar matar dana yan Najeriya, ya mika kansa ga hukumar Yansanda, tare da tabbatar da cewa ya nuna hali nagari, haka zalika ina kira ga jam’iyyarmu ta PDP dasu dauki matakin ladabtarwa akansa, kuma Yansanda su tabbata sun yi abinda ya kamata.” Inji shi.

A wani labarin kuma bincike ya nuna cewa Sanata Ishaku Abbo Cliff yana dauke da cutar sida, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito. An gane haka ne yayin da Sanatan yake neman gurbi a kwalejin horas da jami’an sojan ruwa dake garin Onne na jahar Fatakwal a shekarar 2004, inda hukumar kwalejin ta gano yana dauke da cutar sida, watau AIDS.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng