An rushe gidan da masu garkuwa da mutane suka boye surukin Buhari a cikin birnin Kano
Biyo bayan kubutar da magajin garin Daura, Alhaji Musa Umar, wanda aka sace ranar 1 ga watan Mayu a kofar gidansa a garin Daura, jihar Katsina, bayan sallar Magriba, jami'an tsaro tare da hadin gwuiwar ma'aikatan hukumar tsara birana ta jihar Kano (KANUPDA) sun rushe gidan da aka boye shi tun bayan sace shi.
Masu garkuwar sun boye magajin garin Daura ne a wani gida da ke unguwar Samegu da ke kan hanyar zuwa karamar hukumar Madobi a cikin birnin Kano.
A safiyar ranar Talata ne jami'an 'yan sanda karkashin jagoracin gwarzon dan sanda Abba Kyari da hadin gwiwar abokan aikin sa dake jihar Kano suka gano inda masu garkuwa da mutane suka boye Magajin Garin Daura, wanda yake tsare a wajen su har tsawon wata biyu.
DUBA WANNAN: Matashin Sanata daga arewa ya mammari wata mata saboda ta hantari budurwarsa a sahagon sayar da kayan batsa
Tun a yammacin ranar Litinin har zuwa wayewar garin Talata, jami'an tsaron Najeriya suka yiwa yakin Unguwar Samegu, da ke kusa da Sani Abacha Youth Center a karamar hukumar Kumbotso, tsinke tare da yin musayar wuta da masu garkuwa da mutane suka boye Magajin Garin Daura bayan an gano maboyarsu, wanda daga bisani jami'an tsaron suka yi nasarar kubutar da shi.
Kuma tun daren ranar Litinin aka yi nasarar kama mutum biyu daga cikin wadanda suka yi garkuwar da shi, sannan da safiyar ranar kuma lokacin da aka yi wata musayar wuta da jami'an tsaron suka harbe mutum daya daga cikinsu.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Babban abun takaicin shine yadda su masu garuwar suka shigo cikin jama'a suka kama gidan haya, lamarin da yasa mutane da dama tofa albarkacin bakinsu kan yadda ake bawa mutane gidajan haya ba tare da yin bincike ba, kuma daman tun kwanakin baya ake ta yada rade-radin cewar masu garkuwa da mutanan sun bazamo wasu jihohin arewa ciki har da Kano.
A kwanakin baya ne mutanen garin Daura suka yi addu’o’i domin Allah ya kubutar da Magajin Gari Umaru.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng