Magajin Daura ya isa Abuja, ya samu tarba daga dogarin Buhari

Magajin Daura ya isa Abuja, ya samu tarba daga dogarin Buhari

Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar wanda ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane a ranar Talata, 2 ga watan Yuli bayan ya shafe watanni biyu a hannunsu, ya isa babbar birnin tarayya Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa basaraken ya isa birnin tarayyar ne a cikin wani jirgi mai tashi da saukar ungulu da misalign karfe 1:30 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja.

Daga cikin wadanda suka tarbi basaraken sun hada da dogarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Kanal Muhammed Lawal Abubakar, wanda ya kasance surukinsa.

Sanye da farin kaya, an gano basaraken tare da wasu yaransa da wani mataimakin kwamishinan yan sanda, Abba Kyari.

Sai dai kuma, babu tabbacin ko an kais hi fadar Shugaban kasa, Abuja ko kuma wani gida mai zaman kansa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Ahmed Lawal ya bayyana sabbin shugabannin majalisar dattawa (jerin sunaye)

Idan za’a tuna a ranar 1 ga watan Mayu ne wasu gungun yan bindiga guda hudu suka kai farmaki gidan Magajin garim Daura, inda suka yi awon gaba dashi yayin da yake zaune a kofar gidansa bayan sallar Magariba.

Bayanai sun bayyana akan yadda Yansanda na musamman na IRT dake karbar oda daga babban sufetan Yansandan Najeriya a karkashin jagorancin DCP Abba Kyari suka gudanar da aikin ceton Magajin Gari.

Abba Kyari da tawagarsa sun kaddamar da samame ne a gidan da yan bindigan ke rike da Magajin gari dake Samegu akan hanyar zuwa Madobi a cikin jahar Kano, anan aka dinga musayar wuta tsakanin Yansandan da miyagun.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng