Gwamna Nasir El-Rufai zai fitar da jerin sababbin mukamai

Gwamna Nasir El-Rufai zai fitar da jerin sababbin mukamai

A na sa rai a yau dinnan, 2 ga Watan Yuli, 2019 ne gwamna Nasir El-Rufai zai mika sunayen sababbin kwamishinoninsa a gaban majalisar dokokin jihar Kaduna, kamar yadda mu ka ji labari.

Daily Trust ta samu wannan labari daga majiya mai karfi a Ranar Litinin. Jaridar ta ce labarin da ta samu shi ne, a cikin farkon wannan makon, gwamnan Kaduna El-Rufai zai kafa gwamnatinsa.

Rahoton ya bayyana cewa manyan yaran da gwamnan ya ke ji da su, za su rike ma’aikatu masu tsoka. Haka zalika kwamishinoni kadan da su ka yi a da ne a ke sa rai cewa za su koma kujerunsu.

Har wa yau, labari ya na zuwa mana cewa akwai wadanda su ka rike ma’aikatu da hukumomin jihar da za a iya daga zuwa mukamin kwamishina a sabuwar gwamnatin Malam Nasir El-Rufai.

KU KARANTA: Matasan APC sun fadawa Buhariya guji ba 'Yan adawa Minista

Akwai kuma wasu daga cikin manyan mukarraban gwamnan na APC da za a rike su a cikin fadar gidan gwamnati. Da zarar majalisa ta tantance wadannan Kwamishinoni, za a raba masu wuraren aiki.

Kwanakin baya ne gwamnan ya fitar da sunayen wasu kadan daga cikin wadanda za su rika ba shi shawara. An samu wanda su ka yi aiki a da, da su ka sake komawa matsayin su a wannan karo.

Idan ba ku manta ba a jiye ne Mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu zarcewa a kan mulki, ya fitar da sunayen shugabannin hukumomi da ma’aikatu na jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng