Mufti Menk: Daliban jami'ar Al-Qalam Katsina sun bani kunya matuka wallahi

Mufti Menk: Daliban jami'ar Al-Qalam Katsina sun bani kunya matuka wallahi

- Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan, Mufti Isma'il Menk ya bayyana rashin jin dadin shi akan irin yadda daliban makarantar Al-Qalam Katsina suka nuna rashin da'a a gareshi

- Ya bayyana cewa shi uba ne a garesu, bai kamata ace yana gabatar da karatu kuma suk cika shi da surutu ba

- Rahotanni sun bayyana cewa Malamin ya fara gabatar da karatu a makarantar surutun dalibai yasa dole ya katse karatun ya fita ya basu guri

Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan, wanda yayi suna a kowanne lungu da sako na duniyar nan, Mufti Isma'il Menk ya bayyana cewa daliban jami'ar Al-Qalam dake jihar Katsina sun bashi kunya matuka kan tarbiyar su.

Mufti Menk yayi wannan jawabin ne a daren ranar Lahadi, yayin da aka gayyace shi ya gabatar da lakca da nasihohi a makarantar, kamar dai yadda ya saba gabatar da karatu a makarantu da dama na fadin duniya.

Jaridar Dabo FM ta binciko cewa Mufti Menk ya bayyana wannan kalaman nasa ne na nuna rashin jin dadi, inda ya bayyana cewa dabi'ar daliban ta bashi mamaki mutuka, yadda suka dinga yin surutu a daidai lokacin da yake gabatar da lakca.

KU KARANTA: Allah ya isa: Bayan shafe shekaru 6 muna soyayya, kawai sai nake ganin katin aurenshi da wata - Wata budurwa ta koka

"Wallahi baku yiwa kanku adalci ba, ni a matsayin uba nake a gareku, kuma dole na fada muku gaskiya."

"Gaskiyar magana ita ce kunyi surutu wanda ya wuce tunani, kuma hakan yasa kun bani kunya matuka."

"Saboda haka zan tafi, sai Allah ya kara hadamu watarana idan da rai da lafiya, Allah yayi muku albarka baki dayanku."

Bayan hira da wani dalibin makarantar da yayi da manema labarai, ya bayyana cewa, Malamin ya fara gabatar da lakca ne sai surutun dalibai yayi yawa, hakan yasa dole ya katse lakcar tashi ya fita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel