Sabbin Masarautun Kano: Aminu Ado Bayero ya bayyana dalilin da yasa ya karbi sarautar Bichi
- Mai Martaba Aminu Bayero ya ce bai karbi Sarautar Bichi domin cin mutunci ko rage darajar Sarki Sanusi ba
- Ya ce mutane ne har yanzu basu gane yadda rayuwar take ba, kullum samun canji ake yi
- Ya ce Sarki Sanusi dan uwana ne a gareshi, kuma yana cikin mutane na farko da suka fara yi masa mubaya'a lokacin da ya zama Sarkin Kano
Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce bai karbi sarautar Bichi domin ya ciwa Sarki Sanusi mutunci ko ya rage mishi daraja ba.
Sarkin ya ce hakan ne a wata hira da yayi da manema labarai, inda ya bayyana karbar masarautar ta Bichi ba da niyyar ragewa Sarki Sanusi II daraja ba.
Ya kara cewa ya kamata al'umma su gane cewa a kowanne irin lokaci abubuwa zasu iya canjawa.
"Tun daga kan mahaifinmu a shekarar 1963 da ya karbi mulki abubuwa suke canjawa, kuma haka zasu cigaba da canjawa har abada."
"Misali a nan shine, idan baku manta ba, mahaifinmu ya bani sarautar Dan Majen Kano a shekarar 1990, daga baya na koma Danburan Kano, daga nan na zama Turakin Kano, daga Turaki na zama Sarkin Tsakar Gida, a karshe shine na samu mukamin Wamban Kano."
KU KARANTA: Babbar magana: Ina goyon bayan a bawa 'yan luwadi da madigo 'yancin yin auren jinsi - Amina Mohammed
"Kuma ni ban taba rokarshi wadannan mukaman da yake bani ba."
"Tun daga lokacin da mahaifinmu ya zama Sarkin Kano zuwa lokacin da ya mutu, yayi ta ganin canje-canje kala-kala, kuma duka abinda ya ci karo dashi yana kar barshi hannu bibbiyu.
"Ni a gani na kafa masarautu 5 a jihar Kano ba zai kawo wata matsala a jihar Kano ba, idan har Sarakunan zasu saka bukatar mutanensu a gaba, su hada karfi da karfe, wurin kawo cigaba ga al'umma."
Haka kuma Sarkin yayi tsokaci game da dangantakarshi da Sarki Sanusi, inda ya bayyana cewa babu matsala ko kadan tsakaninsa dashi.
"Sarki Sanusi dan uwana ne, muna ganin girman juna sosai, ni dan sarauta ne, ina cikin mutane na farko da suka fara yi masa mubaya'a lokacin da ya zama Sarkin Kano."
"Saboda haka babu abinda zai canja tsakanina dashi, saboda na zama Sarki, kuma na san ba zai ki bani gudummawa domin nayi abinda ya dace ba."
Idan ba a manta ba watannin da suka gabata ne gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro sababbin masarautu guda hudu a jihar Kano.
Gwamnan ya raba masarautar Kano zuwa masarautu guda biyar, inda ya kara masarautar Gaya, Karaye, Bichi, da kuma Rano.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng