Rukayya Dawayya: Ban cancanci irin sakin da mijina yayi mini ba, saboda ina da matukar kyau da daukar hankalin namiji
- Fitacciyar 'yar wasan Hausa, Rukayya Dawayya ta bayyana cewa ta ji bakin cikin yadda mijinta ya saketa ta hanyar aika mata sakon wayar salula
- Ta ce daga zuwa Kano gaishe da mahaifiyarta wacce kuma ta nemi izinin sa ya yarda, kawai sai taga sako daga gareshi cewa ya saketa
- Ta ce daga baya ta gano cewa mijinta ya auri mata 24 kafin ita, amma saboda tana son aurenta ya dore bata damu ba
Fitacciyar 'yar wasan fim din Hausa, Rukayya Dawayya, ta bayyana irin yadda take jin bakin cikin yadda tsohon mijinta, Adamu Teku ya saketa ta hanyar tura mata sakon wayar salula.
Jarumar ta bayyana hakan ne lokacin da take wata hira da wakilin jaridar Blueprint.
Da take amsa tambayar da dan jaridar yayi mata, akan shin har yanzu tana dana sanin auren tsohon mijin nata Adamu Teku, wanda daman tun kafin tayi auren sai da aka yi mata gargadi akan kada ta aure shi, saboda halin shi na auri saki.
Jarumar ta bada amsar cewa: "A matsayina na Musulma, ina ganin nadama ba ita ce amsar da ya kamata na bayar ba, amma zancen gaskiya har yanzu ina jin ciwon yadda ya sakeni ta hanyar aiko mini sako tes ta wayar salula.
KU KARANTA: Babbar magana: Daga yin wasa da lamarin aure Zainab da Sunusi sun angwance a shafin Facebook
"Akwai ranar da mahaifiyata ta dawo daga Saudiyya, sai na nemi izinin naje na gaida ita a Kano, sai ya amince naje na gaida ita.
"Na tashi na wuce Kano ni da dana Arafat, dana zo Kano na yi ta kiran wayarshi yaki dagawa na tura sakon tes babu amsa. Sakon shi dana gani na karshe shine wanda ya rubuto cewa ya sakeni saki uku.
"A matsayina na 'ya mace, hakan wani abu ne mai matukar ciwo a rayuwata. Ban cancanci irin wannan sakin daga gurin mijina ba, saboda ina da matukar kyau da daukar hankalin duk wani da namiji.
"Bayan na auri Adamu Teku, na gano wasu abubuwa dangane da rayuwarshi, amma duk da haka na jure zama dashi saboda ina so aurena ya dore."
Jarumar ta bayyana cewa ta gano cewa tsohon mijin nata kafin ya aureta sai da ya auri mata 24, sannan yana da 'ya'ya guda tara wadanda duka ba uwarsu daya ba, ciki kuwa harda mace babba wacce ta zama kawa a gareni.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng