Nayi iya bakin kokarina domin magance matsalar tsaro a jihar Zamfara - Yari

Nayi iya bakin kokarina domin magance matsalar tsaro a jihar Zamfara - Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, a ranar Litinin, 1 ga watan Yuni ya kare kansa akan batun tsaro a jihar, inda yake fadin cewa yayi iya kokarinsa wajen magance matsalar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa Yari ya bayyana hakan ne a Talata Marafa a wata ganawa da shuwagabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga yankunan kananan hukumomin Gusau, Maradun, da Tsafe suka yi.

Yace: “Ina mai amfani da wannan damar a madadin mambobin APC a jihar Zamfara don yin jaje ga mutanen kananan hukumomin Maradun da Tsafe bisa hare haren da yan bindiga suka kai kauyukan su.

“Muna addu’a ga Allah madaukakin Sarki da ya gafarta nma wadanda suka rasa rayukansu Ya kuma kara ma iyalansu hakurin rashin.

“Kun san a lokacin gwamnatina, nayi iya kokarina don magance matsalar, ko da yake wasu mutane suna zarginmu da cewa bamu yi kokari ba wajen magance lamarin.

“Bamu fadi haka ba ko saboda muna jin dadin abun dake faruwa, amman ya kamata mutane su daina yanke hukunci bisa ra’ayin kansu ko na siyasa."

Tsohon gwamnan yace, “Kamar yanda nake fadi a kullun, lamarin rashin tsaro ya wuci ra’ayin kai ko na siyasa, mu mara ma shugaban kasa Buhari baya wajen yaki da ta’addancia jihar”.

Yari har ila yau ya roki mutanen jihar da su cigaba da gabatar da addu’a tare da neman Allah ya shiga lamarin don kawo karshen matsalar.

Yayin da yake bayyana ra’ayinsa a taron, Shugaban karamar Hukumar Maradun, Alhaji Ahmad Abubakar yace kalubalen da harkar tsaro e fuskanta a yankin ya karu.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Ganduje da Sanusi: Sheikh Dahiru Bauchi ya nemi karin mutane su shiga cikin lamarin

A cewar shi, an kai hari kauyuka da dama a watan da ya gabata, inda aka kaddamardahari kusan kullun a ciin mako da ya gabata.

Takwaransa na karamar hukumar safe, Alhaji Aminu Mudi yayi godiya ga tsohon gwamnan kan damuwa da ya nuna akan mutanen jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng