Kai jama’a: Uwargida ta farka kirjin Maigidanta da wuka

Kai jama’a: Uwargida ta farka kirjin Maigidanta da wuka

Rundunar Yansandan jahar Anambra ta sanar da kama wata mata yar shekara 20 mai suna Makoduchukwu Ndubuisi wanda ake zarginta da halaka mijinta John Bosci Ngu dan shekara 35, inji rahoton jaridar Sahara.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari mai muni ya faru ne a kauyen Nsugbe dake cikin karamar hukumar Anambra ta gabas, kamar yadda kaakakin Yansandan jahar, Haruna Muhammad ya tabbatar.

KU KARANTA: Shugabancin majalisa: Akwai jikakkiya tsakanin Ganduje da Oshiomole

Kaakaki Muhammad ya bayyana cewa “A ranar Asabar, 29 ga watan Yuni da misalin karfe 8 na safe Yansandan garin Onitsha suka kama wata mara mai suna Makoduchkwu Ndubuisi akan zargin kashe mijinta.

“Wannan lamari ya faru ne a sanadiyyar wata yar sabani da suka samu a tsakaninsu, wanda har ta kaisu ga dambacewa, ana cikin haka ne matar ta samu dama ta daba masa wuka a kirji, har ta farka kirjin.

“Ba tare da bata lokaci ba Yansanda suka isa inda lamarin ya auku, inda suka garzaya da John Bosci zuwa Asibiti cikin mawuyacin hali, a can ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa, a yanzu mun ajiye gawarsa a Asibitin kuma an kaddamar da bincike akan lamarin.” Inji shi.

A wani labarin kuma, har yanzu ba’a warware bahallatsar data dabaibaye yunkurin kashe mijinta da wata amarya mai suna Hanan ta yi a jahar Kano ba, inda ya luma masa wuka a cikim har sai da yan kayan hanjinsa suka bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel