Sojoji sun kama 'yan bindiga 25, sun kwato makamai masu yawa (Hotuna)

Sojoji sun kama 'yan bindiga 25, sun kwato makamai masu yawa (Hotuna)

Dakarun Sojojin Najeriya da ke atisayen Operation Harbin Kunama III sun yi nasarar kama kungiyoyin 'yan bindiga da dama da ke adabar garuwuwan Isa, Rabbah da Burkusuma da garuruwan da ke kusa da Dajin Sububu a Sokoto da Batsari, Safana da Kankara a Dajin Dumburum da ke jihar Katsina.

Kazalika, Dakarun Sojin da aka girke a Super Camp da ke kusa da Bena, Jega, Danko da Wasagu sunyi artabu da 'yan bindiga da dama kuma sun lalata mabuyar 'yan bindigan 5 a Dajin Gando da ke jihar Kebbi.

A yayin da ya ke yi wa manema labarai bayani kan ayyukan rundunar, Babban kwamanda mai bayar da umurni (GOC) a Division 8, Manjo Janar Hakeem Otiki a ranar 26 ag watan Yunin 2019 ya ce sun lalata mabuyar 'yan bindiga biyar kuma sun lalata babura 25 a sumamen da suka kai.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 8, sun kama 'yan leken asirin 'yan bindiga 17 a Sokoto

Ya kara da cewa Sojojin da aka girke a jihohin Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara suna samun nasarori a yakin da suke yi da 'yan bindiga tare da taimakon Sojojin Saman Najeiya (NAF).

GOC din ya ce abubuwan da aka kwato sun hada da bindigu, alburusai, bindigun farauta da sauransu.

Ya tabbatarwa mazauna garuruwan cewa Rundunar Soji a shirye ta ke domin bayar da cikaken tsaro gare su tare da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.

Ya yi amfani da damar wurin jinjinawa jaruman dakarun sojojin Najeriya bisa bajintar da suke nuna wa a filin daga, ya kuma mika godiyarsa da yan kungiyar sa kai da mafarauta da sauran al'umma da ke taimakawa sojojin da bayyanai masu amfani.

Sojoji sun kama 'yan bindiga 25, sun kwato makamai masu yawa
'Yan bindiga da baburan su da Sojojin Najeriya suka kama
Asali: Twitter

Sojoji sun kama 'yan bindiga 25, sun kwato makamai masu yawa
Wasu bindigu da kayan 'Yan sanda da aka kwato hannun 'yan bindiga
Asali: Twitter

Sojoji sun kama 'yan bindiga 25, sun kwato makamai masu yawa
Baburan da Sojojin suka kwato hannun 'yan bindiga
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: CBN za ta rage yawan kudaden da ke kewayawa a Najeriya, ta bayar da dalili

Sojoji sun kama 'yan bindiga 25, sun kwato makamai masu yawa
Sojoji sun kama 'yan bindiga 25, sun kwato makamai masu yawa
Asali: Twitter

Sojoji sun kama 'yan bindiga 25, sun kwato makamai masu yawa
Bindigu da sojoji suka kwato hannun 'yan bindiga
Asali: Twitter

Sojoji sun kama 'yan bindiga 25, sun kwato makamai masu yawa
Sauran makamai da dakarun sojojin Najeriya suka kwato hannun 'yan bindiga
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164