Tallafin 5,000: Gidaje 54,000 za su amfana daga shirin gwamnatin Buhari a jihar Zamfara

Tallafin 5,000: Gidaje 54,000 za su amfana daga shirin gwamnatin Buhari a jihar Zamfara

- Anyi wa akalla gidaje 54,197 rijista domin karban tallafin N5000 daga gwamnatin tarayya a jihar Zamfara

- Wadanda za su amfana daga shirin za su rika samun kudin ne a duk wata daga kudaden da gwamnati ke turawa kai-tsaye a asusun ajiyar su na banki

- Shirin na daya daga cikin tsare-tsaren tallafawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da shi, kuma ta ke wa talakawa wajen rage musu radadin kuncin rayuwa

Akalla gidaje 54,197 aka yi wa rajista domin karbar tallafin naira 5,000 kai-tsaye daga Gwamnatin Tarayya a Jihar Zamfara.

Jagorar shirin ta Kasa, Temitope Sinkaiye ce ta bayyana hakan a Gusau, babban birnin Jihara ranar Juma’a, 28 ga watan Yuni a wajen taron yi wa jami’an shirin bitar kwana daya da aka gudanar.

Sadiya Abdullah i daya daga cikin manyan jami’an shirin ta kasa da ta wakilci Temitope, ta ce za su rika samun kudin ne a duk wata daga kudaden da gwamnati ke turawa kai-tsaye a asusun ajiyar su na banki.

Ta kara da cewa an zabi Kananan Hukumomin Anka, Bungudu, Birnin-Magaji, Kaura-Namoda, Tsafe da Talata Mafara a matsayin inda za a fara cin moriyar shirin.

Ta ce shirin na daya daga cikin tsare-tsaren tallafawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da shi, kuma ta ke wa talakawa wajen rage musu radadin kuncin rayuwa.

“Za a bayar da naira 5,000 ce, amma kuma za a bayar da na wata biyu a lokaci guda, domin kudin su zamana sun isa wanda aka bai wa ya yi tattalin samun fara ajiye dan wani abu daga ciki domin tattalin dogaro da kai.

Daga karshe ta ce a yanzu an samu jami’an kula da tura kudaden har su 137 a cikin kananan hukumomin shida da za a fara da su.

KU KARANTA KUMA: Ka fito filli ka bayyanawa 'yan Najeriya kadarorinka - PDP ta kallubalanci Buhari

Jami’an da suka wakilci gwamnatin Jihar Zamfara sun nuna farin cikin fara wannan shiri a jihar. Sannan kuma sun sha alwashin cewa gwamnatin jihar za ta bada goyon baya da hadin kai wajen ganin an cimma nasarar shirin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng