Tirkashi: A karon farko Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana akan hana Almajiranci da ake shirin yi

Tirkashi: A karon farko Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana akan hana Almajiranci da ake shirin yi

- A karon farko kenan Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi magana dangane da hana Almajiranci a Najeriya

- Malamin ya ce bai ga dalilin da zai sa ace abinda aka shafe sama da shekara dubu ana yi ba ace dare daya za a hana yin shi

- Idan ba a manta ba a satin da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada sanarwar cewa zai kawo karshen Almajiranci a kasar nan

Shugaban kungiyar Dahiru Usman Bauchi, Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru ya ce ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake tunani game da cewar zai hana Almajiranci a Najeriya.

Alhaji Dahiru da yake magana da manema labarai a Bauchi, ya mai da martani game da maganar da mai bawa shugaban kasa shawara a fannin tsaro yayi ta cewa gwamnatin tarayya na shirin sanya dokar hana almajiranci a kasar nan.

Dahiru ya ce: "Ana Almajiranci fiye da shekaru 1,000 da suka wuce a kasar nan, kuma hakan bai sa ya zama matsala a fannin tsaron kasar nan ba, daliban suna koyan karatu ta fannin karanta Al-Qur'ani da kuma haddace shi, kuma hakan ba wai ya mayar da su 'yan ta'adda ba ne, hasali ma sune suke yiwa kasa addu'ar neman zaman lafiya."

Ya kara da cewa, "Duk cikin wadannan 'yan ta'addar da ake kamawa a kasar nan babu Almajiri ko daya, duka 'yan fashi ne, sai masu garkuwa da mutane da sauran 'yan ta'adda."

KU KARANTA: Babbar magana: Bakin jahilci ne wani jahili ya ce azumin 'Sittu Shawwal' ba Sunnah bane - Bin Uthman Kano

"Mun sha ganin 'yan sanda suna bincike akan 'yan ta'addar da suke kamawa, idan suka tambayesu cewa sunyi karatun Al-Qur'ani ko kuma sunje makarantar Allo, amsar da suke basu ita ce aa."

"Ina ganin lokaci yayi da ya kamata gwamnati ta banbance tsakanin 'yan ta'adda da Almajirai, su ba 'yan ta'adda bane karatun addini kawai suke yi kuma suke haddace Al-Qur'ani mai girma."

Ya kuma shawarci masu fada aji a kasar nan da su cigaba da addu'ar neman zaman lafiya da kwacinyar hankali, inda ya kara da cewa, "Babu ta hanyar da zaku hada Almajiri da 'dan ta'adda, hakan ba daidai bane, kuma ba gaskiya bane."

"Muna addu'ar Allah ya zaunar da kasar mu lafiya, ya kuma bai wa shugabannin mu damar mulki cikin kwanciyar hankali da amana, kuma muna yiwa shugaban kasa addu'ar samun koshin lafiya domin cigaba da gabatar da mulki yadda ya kamata," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel