N/Castle da Chelsea za su yi hayar Mourinho da Lampard, Barce za ta maida Neymar

N/Castle da Chelsea za su yi hayar Mourinho da Lampard, Barce za ta maida Neymar

A daidai lokacin da a ke cigaba da cin kasuwar sayen ‘yan wasa a cikin Nahiyar Turai, mun fara samun wasu rade-radi da za su masu kallon kwallon kafa mamaki, muddin su ka tabbata a yanzu.

Daga cikin wannan rade-radin ciniki da a ke yi akwai:

1. Lampard ya koma horas da Chelsea

Ana tunani Frank Lampard zai dauki aikin da Maurizio Sarri ya ajiye na horas da kungiyar Chelsea da ya bari a baya. Yanzu Chelsea ta nemi dama wajen kungiyar Derby County wajen tattaunawa da Kocin. Babu mamaki Chelsea ta biya Derby kudi ta dauki Lampard a makon nan.

KU KARANTA: Ya samu aiki saboda tsabar kaunar 'Dan wasa Lionel Messi

2. Jose Mourinho zai tsaya a Firimiya

Akwai manyan alamu da ke nuna cewa tsohon Kocin Chelsea da Manchester United watau Jose Mourinho zai iya komawa Newcastle. Tun kwanaki a ka fara wannan rade-radi, amma yanzu ya yi karfi bayan ta tabbata cewa Rafael Benitez zai bar kungiyar a karshen wannan Watan.

3. Neymar na iya komawa Sifen

Wani cefane da za a iya gani mai ban mamaki shi ne PSG ta saidawa Barcelona ‘Dan wasa Neymar Jr. da ta saya kwanaki. Idan ta tabbata Neymar zai koma Sifen, dole ya hakura da makudan albashin da ya saba karba. Da alamu zai yi wuya Neymar ya cigaba da zama a PSG.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel