Tirkashi: Babu abinda ta iya sai fita yawon ta zubar da neman maza - Inji mijin da matarsa ta cakawa wuka a Kano

Tirkashi: Babu abinda ta iya sai fita yawon ta zubar da neman maza - Inji mijin da matarsa ta cakawa wuka a Kano

Lamarin abunda ya faru a tsakanin matar da ta caka ma mijinta wuka da shi kanshi mijin a jihar Kano na dada zama abin kunya.

Hotunan da suka bayyana sun nuna yadda sashin jikin Fatima Hanan Hamza ke cike da raunuka wanda ake zargin mijinta neya azabtar da ita.

Sai dai kuma a yanzu mun samu labarin cewa mijinta da ake zargi yana muzuna mata, Saeed Hussain yayi magana akan lamarin sannan kuma lamarin na dada munana.

A cewar hirar da aka yi da Saeed, Hanan bata taba son shi ba kuma gaba daya auren ma na hadi ne wanda mahaifiyar Hanan tayi. Ana zargin cewa hakan ne ma ya sanya mahaifiyarta yin Allah wadai da ita akan lamarin daba ma mijinta wuka da tayi.

An tattaro daga majiya cewa “mahaifiyar ta sai ta matsa aka sake dawo da maganar don shi da yaga haka ma har ya rabu da ita, toh daga baya dai akazo akayi aure bisa tunanin ko Allah zaisa daga baya ta dawo tana son shi. Sai dai bayan aure sabanin haka ce ta rika aukuwa, domin cikin watanni shiddan nan babu wani cigaba da aka samu hasalima a koda yaushe sa’in sa kawai suke samu a tsakanin su.”

Wani babban bayani kuma shine cewa Saeed, wanda ya kasance ma’aikaci na jiha da jiha wanda ke zama a Gusau, yayi zargin cewa Hannan tana kawo maza gida.

Yace: “Kaga dai ni ba ma a garin nan nake zaune ba a Gusau (Zamfara) nake aiki na, sai na dan samu sarari haka sai in dawo hutu gida wajen mata ta, amma daga baya sai na samu cikakken bayani daga majiya mai tushe na cewa ita mata ta (Hanan) tana kawo maza idan bana nan, daga bisani sai kuma na gano cewa ta hada baki da wasu masu gadi na su biyu wadanda su suke boye min wannan al’amari a duk sa’adda nayi kokarin tabbatar da zargin da nakeyi.

“A lokacin da na tabbatar da wannan al’amari sai na kori wadannan masu gadi biyu da take hada baki dasu na bar mata daya, na kwace wayoyin ta na kuma gargade ta sosai akan wannan dabi’a tata, sai dai hakan baisa ta daina ba,” inji Sa’idu.

Ya ci gaba da cewa: “Haka nan muka cigaba da zama cikin wannan matsala domin ni nasawa raina aure cike yake da kalubale, toh amma ita a nata tunanin kawai na hana ta sakewa ne."

Yayin da yake magana kan abun da ya faru cikin daren, wanda ake zargin yayi ikirarin cewa, harin ya faru ne tsakar dare kuma ta ji rauni a lokacin da yayi yunkurin kwatar wukan daga hannun ta sai yace: “Rannan ina kwance karfe 12 na dare naji ana ta kawo min suka da wuka, ashe wai mata ta ce ta farmin da suka da wuka, a nan na kamata da kokawa domin inga na kwace wukar dake hannun ta amma tuni tayi nasarar zurma min a ciki har saida kayan ciki na suka zazzago, haka dai nayi ta kokawa da ita har saida ta sake yanka ta, a garin kokarin kwace wukar ne ta daki gefen gado ta kurje a jikin ta.

“Ganin na kwace wukar ne na ruga waje da gudu nasa mai gadi ya rufe gida karya barta ta fita, ni kuwa muka kama hanyar asibiti da makota wadanda suka suka rarrafa dani zuwa asibiti, haka muka dangana ni kuwa na toshe kayan ciki na da suka zazzago da hannu.”

KU KARANTA KUMA: Dan kasuwa, Alhaji Umar, ya kai tsohuwar matarsa kotu saboda ta ki fita daga gidansa

Da aka bukace shi ya bayyana ra’ayinsa kan zargin cewa ya kasance mai wulakanta matarsa, ya karyata hakan, ya kuma yi ikirarin cewa ta fadi hakane don ta kare kanta daga laifin da ta aikata.

An rahoto yana mai cewa: “Wannan ta fada ne kawai watakila saboda ta kare abinda tayi, amma dai ina son in tabbatar maka da cewa ban taba dukan mata ta ba kuma kamar yadda na gaya maka tunda farko ni fa nake son ta ita bata so na, kuma hasali ma ina da kyamarar nadar bayanan sirri ta CCTV a gidan tana daukar komai, za’a iya dubawa a gani.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel