An kashe mutum 3, anyi garkuwa da 20 sannan an sace dabbobi 500 yayinda yan fashi suka kai mamaya kauyukan Zamfara

An kashe mutum 3, anyi garkuwa da 20 sannan an sace dabbobi 500 yayinda yan fashi suka kai mamaya kauyukan Zamfara

- An kashe mutane uku a sabon harin da aka kai karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara

- A halin, mutane 20 sun jikkata sannan an sace dabbobi 500 yayinda yan fashi suka kai farmaki kauyuka daban-daban a Zamfara

- Kauyukan da harin ya shafa sun hada da Faru, Bachiri da kuma Gama Giwa

Rahotanni sun kawo cewa an kashe mutane uku yayida aka yi garkuwa da kimanin mutane 20 biyo bayan sabon harin da aka kai karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara.

Mutane da dama sun jikkata sannan anyi fashin dabbobi 500 a harin wanda ya gudana a mahaifar Gwamna Bello Matawalle.

A cewar Shugaban kasaramar hukumar, Ahmed Abubakar, yan fasin sun kai mamaya kauyen Faru a ranar Litinin da ya gabata da kuma Bachiri a ranar Asabar yayinda aka kai wani hai kauyen Gama Giwa a ranar Lahadi.

KU KARANTA KUMA: Biliyan 2.3 Gwamna Abubakar ya kashe wajen birne gawa – Bala Mohammed

Mista Abubakar yace: “Karamar hukumata na karkashin mamaya, suna ta kai hare-hare garuruwanmu da kauyukanmu a kullun sannan sojoji ba za su iya shan kan wadannan mutane ba. Muna samun hare-hare hudu zuwa biyar a duk mako, mutane na mutuwa, sannan ana garkuwa da wasu saboda hukumomin tsaro basu da kayayyakin aiki na yakar wadannan mutane.”

Duk kokari da aka yi na jin tab akin jami’an Operation Sharen Daji bai samu ba, sai dai Shugaban ya sanar da Channels Television cewa a yanzu mazauna kauyukan na komawa hedkwatar karamar hukumar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng