Matar aure ta caka wa mijinta wuka a fuska watanni 7 bayan daurin aure a Kano

Matar aure ta caka wa mijinta wuka a fuska watanni 7 bayan daurin aure a Kano

Wani dan Najeriya mai suna Saeed Hussain yana kwance rai hannun Allah a Asibitin Koywarwa na Aminu Kano da ke jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa an garzaya da Hussain zuwa asibiti ne a daren Juma'a 21 ga watan Yuni bayan matarsa da aka daura musu aure watanni bakwai da suka shude, Hanan, da caka masa wuka yayin musayar yawun baki.

Hussain, wanda ya kammala karatun lauya daga Jami'ar Bayero ta Kano ya auri Hanan ne a watan Disambar 2018.

DUBA WANNAN: Da duminsa: An kama kwararen mayaki na kasa da kasa cikin 'yan Boko Haram a Borno

An samu rashin jituwa tsakanin ma'auratan ne a gidansu da daren ranar Juma'a kuma daga baya abin ya janyo dambe. A yayin damben ne Hanan ta dabawa mijinta wuka a fuskarsa.

Tuni dai hukuma sun kama Hanan kuma ana gudanar da bincike kan lamarin.

Daya daga cikin abokanan Hussain, ya bayyana cewar matar Hussain ne ta daba masa wuka kuma ya roki al'umma su taya su da addu'an samun sauki duba da cewa abokin nasu yana kwance a asibiti inda ake bashi kulawa.

Amarya ta caka wa mijinta wuka watanni 7 bayan daurin aure a Kano
Amarya ta caka wa mijinta wuka watanni 7 bayan daurin aure a Kano
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel