Kungiyar AYCF ta fadi dalilin ta na son dan arewa ya cigaba da mulkin Najeriya a 2023

Kungiyar AYCF ta fadi dalilin ta na son dan arewa ya cigaba da mulkin Najeriya a 2023

- Alhaji Yerima Shettima ya ce arewa ce za ta fita da shugaban kasa a 2023 bayan Buhari kammala wa'adin mulkinsa

- Shettima, wanda shine shugaban kungiyar Arewa Consultative Forum (AYCF) ya ce gwamnati mai ci yanzu ba ta yiwa arewa gata

- Shettima ya ce arewa ba za ta taba barin mulki ya kubce mata ba saboda bayan shi babu wani abu da ta ke da shi

Shugaban kungiyar Arewa Consultative Forum (AYCF), Alhaji Yerima Shettima ya ce yankin arewa ne za ta fitar da shugaban kasa bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa'adinsa a 2023.

Legit.ng ta gano cewar Shettima ya yi wannan jawabin ne cikin wata hira da akayi da shi a jaridar New Telegraph a ranar Juma'a 21 ga watan Yunin 21.

DUBA WANNAN: Rikicin jam'iyya: Ana fargabar za a sake dakatar da wani gwamnan APC

Shugaban na AYCF ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta tsinanawa yankin arewa komai ba inda ya ce gwamnatin mai ci yanzu ta mutanen mazabar kudu maso yamma ne.

Ya ce: "Ban san wanda zai zama shugaban Najeriya na gaba ba sai munga wadanda za su fito takara. Sai dai idan ana maganar yankin da zai fitar da shugaban kasa a 2023. Na dade ina nanatawa cewa Arewa ce za ta fitar da shugaban kasa kuma kamar yadda ka ke gani abin na fitowa fili.

"Bana tsokaci a kan abinda banda tabbas a kansa. Mun tabbatar cewa wannan gwamnatin ba ta tabukawa 'yan arewa komi ba. Wannan gwamnan na yankin Kudu Maso Yamma ne. Su ne suka kwashe komai."

Shettima ya kuma ce Shugaba Muhammadu Buhari ne kadai ya ke rike da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma jam'iyyar za ta rushe kafin shekarar 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164