Sabon Manajan NNPC: Muhimman abubuwa guda 9 da ya kamata ku sani dangane dashi

Sabon Manajan NNPC: Muhimman abubuwa guda 9 da ya kamata ku sani dangane dashi

A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa Mele Kolo Kyari mukamin manajan darakta (GMD) na kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC)

Yana da mutukar muhimmanci mutane su san wanene Mele Kyari, tunda shine zai rike ragamar bangaren da yafi kowanne muhimmanci a bangarorin da suke kawowa Najeriya kudi.

Ga wasu muhimman abubuwa guda tara dangane da sabon manajan daraktan:

1. Tsohon ma'aikacin OPEC

Kyari tsohon ma'aikacin kamfanin hako man fetur na OPEC ne. Ya jagoranci ma'aikatar a bangaren kula da kasuwar man fetur ta duniya.

2. Tsohon manajan danyen mai

Kafin a bashi mukamin OPEC, Kyari yayi shugaban kungiyar hako danyen mai, hakan ya nuna cewa ya jima yana aiki a bangaren mai.

3. Ya fara aiki a bangaren mai a shekarar 1988

Sabon daraktan NNPC ya fara aiki a bangaren man fetur a bangaren binciken mai shekarar 1988 zuwa 1991, kafin daga baya ya canja fanni ya koma bangaren IDSL.

4. Kyari yana da kwarewa a bangaren aikin mai

Sabon manajan man fetur din yayi aiki a ma'aikatar hada-hadar man fetur ta (NAPIMS) a shekarar 1998, sannan ya zama shugaban kamfanin na babban birnin tarayya.

5. Yayi aiki a bangarori da dama a kamfanin NNPC

Yayi aiki a bangarori da dama a kamfanin NNPC daga shekarar 2007 zuwa yanzu.

KU KARANTA: Jerin halaye guda 8 na Manzo Allah (S.A.W) wadanda Yahudu da Nasara suka aminta da su

6. Manaja a bangaren hada-hadar danyen mai

Yayi aiki a matsayin manaja, a bangaren hako danyen mai daga shekarar 2008 zuwa shekarar 2014 daga nan ya zama janar manaja a bangaren kasuwar hada-hadar danyen mai.

7. Kyari yana da digiri a fannin ma'adanai

Yayi karatun digiri din shi a fannin ma'adanai a jami'ar Maiduguri a shekarar 1987.

8. Zai shiga ofis a farkon watan Yuli

Kyari shine manajan darakta na 19 a kamfanin man fetur na Najeriya, kuma zai fara aikin shi a ranar 8 ga watan Yuli.

9. Kyari yayi aiki kwarai da gaske a lokacin da yake aiki a wurin danyen mai

Lokacin da yana bangaren kasuwanci na danyen mai, an samu cigaba sosai a kamfanin.

Wannan shine kadan daga cikin muhimman abubuwa da ya kamata ku sani dan gane da sabon manajan darakta na kamfanin man fetur na kasa (NNPC), Mele Kolo Kyari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng