Bashir Ahmad Ya Samu Babbar Kujera a Kwamitin Yakin Neman Zaben Abba a Kano
- Bashir Ahmad ya sanar da karbar nauyin jagorantar sashen yada labarai na zamani na kwamitin yakin zaben APC a Kano
- Tsohon hadimin shugaban kasar zai yi amfani da gogewarsa a yakin neman sake zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Ya ce za su yi amfani da fasaha da kafafen sada zumunta wajen yada nasarorin gwamnatocin APC a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Kano ta nada Bashir Ahmad cikin ‘yan kwamitin yakin neman zabe a 2027.
Hadimin na tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi wa APC aiki a zaben gwamna da na shugaban kasa.

Source: Facebook
APC ta hada Bashir Ahmad da kamfe a Kano
Kamar yadda ya sanar da kan shi a kafar X a farkon makon nan, Bashir Ahmad ya tabbatar da zai koma gida domin kamfe.

Kara karanta wannan
Sanata ya tabbatar da abin da ake tsoro a APC, ya ce akwai matsaloli cikin jam’iyyarsu
Matashin ‘dan siyasar ya ce an nada shi a matsayin Darektan kwamitin kirkira da yada labarai na zamani na kamfe.
'Dan siyasar da ya yi fice a dandalin sada zumunta mutumin karamar hukumr Gaya ne daga kudancin Kano.
Sauran 'yan kwamitin yakin neman zaben a Kano
Bashir ya bayyana sauran ‘yan siyasa da kwararru da zai yi aiki da su wajen sauke wa jam’iyyar APC wannan nauyi.
Ibrahim Adam wanda mai taimaka wa Gwamnan jihar Kano ne a wannan bangare shi ne mataimakin darekta na I.
Musayyib Kawu Ungogo mai shugabantar gidan dabbobi shi aka zaba ya zama mataimakin darekta na II kwamitin.
Aminu Dahiru, Auwal Kingdom suna cikin mataimakan darektocin kwamitin tallar Abba a kafofin sadarwa na zamain.
Sauran wadanda jam’iyyar APC ta dauko su ne Amir Abdullahi Kima da Khadija Aminu Shariff da ita kadai ce mace.
Sanarwar karbar mukamin da Bashir Ahmad ya fitar
Malam Bashir mai shekaru 35 ya fitar da bayani a Facebook dangane da yadda za su yi aiki.
"Ina farin cikin karbar nauyin jagorantar Daraktan Yada Labarai na Zamani da kirkire-kirkire na yakin neman sake zaben Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf a shekarar 2027.
"Manufarmu ita ce amfani da kafafen yada labarai na zamani, fasaha da kirkire-kirkire wajen hulda da al’ummar Jihar Kano, tare da yada nasarorin gwamnati yayin da muke kokarin ganin an sake zaben AKY a wa’adi na biyu.
"Za mu samar da ingantacciyar kafa ta zamani da za ta hada gwamnati da jama’a, ta sanar da su ci gaban da ake samu, tare da jawo goyon bayansu ga Gwamna.
"Wannan kira ne na hidima, kuma a shirye muke mu bayar da gudummawarmu."
- Bashir Ahmad
Bashir Ahmad ya kare sanarwar da lagon da gwamnati ta dauko n Kano First, wato jihar aka sa a gaba ba wani mutum ba.
Abba zai rantsar da kwamitin ranar Alhamis
A ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba 2026 gwamna Abba Kabir Yusuf zai rantsar da ‘yan kwamitin na kamfen 2027.
Darektan kwamitin ya ce za su yi aiki da majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na APC domin nasarar Abba.
Za kuma su hada kai da City Boy Movement, Arewa for Asiwaju, Abba Go Again Movement, AbbaGaro da sauran kungiyoyi.
Kwankwaso ya yi batun dawo da tallafin mai
An rahoto cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya tabo zancen tallafin mai a gwamnatin NDC idan sun ci zaben shugaban kasa.
Madugu na darikar Kwankwasiyya ya ce jagororin jam’iyyarsa sun yarda cewa farashin makamahi ya yi tsada sosai a yanzu.
Sanata Kwankwaso ya ce NDC na iya dawo da tallafin fetur domin rage farashin mai bayan an yi watsi da tsarin a Mayun 2023.
Asali: Legit.ng

