An yi ganawar sirri tsakanin gwamna Zulum da Buhari

An yi ganawar sirri tsakanin gwamna Zulum da Buhari

An yi wata takaitacciyar ganawar sirri tsakanin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da sabon gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a fadar shugaban kasa, Villa, da ke Abuja.

Babu wata sanar wa ko jawabi dangane da dalilin ganawar daga bangaren fadar shugaban kasa ko kuma gwamnatin jihar Borno.

Wasu masu bibiyar al'amuran kasa na ganin cewar ganawar ba zata rasa nasaba da yawaitar hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram ba a 'yan kwanakin baya bayan nan.

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai munanan hare a sassan jihar Borno a cikin satin nan.

Ko a yau, sai da Legit.ng ta kawo labarin cewar a kalla jami'an sojin Najeriya 18 suka rasa rayukansu yayinda 6 suka jikkata bayan harin da yan kungiyar Boko Haram suka kai barikin soji dake Gajiram, karamar hukumar Nganzai dake jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan mumunan hari ya auku ne misalin karfe 4:30 na yamma ranar Litinin, majiya daga gidan soja ya bayyana cewa har yau laraba ana cigaba da kirga abubuwan da aka rasa sakamakon harin.

Majiyar ta kara da cewa manyan kayan yaki hudu daban-daban da manyan bindigogi yan Boko Haram suka sace.

A ranar Talata ma Legit.ng ta wallafa wani labarin cewa a kalla dakarun sojin Najeriya biyar ne suka rasa ran su bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari a wani sansanin soji da ke Monguno a jihar Borno.

An kai harin ne da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Litinin. Wata majiyar soji ta shaida wa jaridar SaharaReporters cewar mayakan sun dira a sansanin sojin a cikin motoci kusan 30 dauke da muggan makamai, kuma sun ci karensu babu babbaka kafin daga bisani a turo karin wasu dakarun sojin.

Kafin isowar karin rundunar sojin, mayakan kungiyar sun yi awon gaba da bindigu da alburusan sojoji tare da saka wuta a sansanin sojin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel