Wata sabuwa: Shaidan ne ke hada Sarkin Kano da Ganduje rigima - Attahiru Bafarawa

Wata sabuwa: Shaidan ne ke hada Sarkin Kano da Ganduje rigima - Attahiru Bafarawa

- Bafarawa ya ce bai kamata ace manyan arewa su zuba ido suna gani jihar Kano na neman rugujewa ba

- Ya bayyana cewa a yanzu inda Buhari zai kira su ya tsawatar da su shikenan magana ta mutu babu wanda zai kara taso da ita

- Bafarawa ya bayyana cewa kamata yayi a hada kwamiti ta manyan arewa, wadanda za su tsaya tsayin daka wurin ganin sun sulhunta rikicin shugabannin biyu

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Dalhatu Attahiru Bafarawa ya soki al'amarin manyan arewa na shirun da suka yi dangane da rikicin masarautar Kano, inda ya bayyana cewa hakan na iya zama matsala ga daukacin kasar nan baki daya.

"Wannan rikici na kano ba rikicin jihar Kano ba ne kawai, rikici ne na yankin arewa baki daya, kuma abinda ya shafi yankin arewa tamkar ya shafi kasa ne baki daya."

Bafarawa ya kara da cewa: "Irin wadannan mutane suna samun rikici a junansu, kuma ace babu wani babban mutum da zai fito a cikin dattijan arewa da zai yi musu magana, mu da muke da Sarkin Musulmi, Sarkin Zazzau da Shehun Borno, manyan sarakuna da malamai."

Rikicin jihar Kanon ya samo asali ne bayan an raba masarautar Kano zuwa gida biyar, sannan kuma gwamnatin jihar tana binciken fadar Sarkin Kano da laifin handame wasu biliyoyin kudi, wanda tayi amfani da su ba bisa ka'ida ba.

KU KARANTA: Magani a gonar yaro: Magunguna 18 da Zogale ke yi a jikin Dan Adam

Tsohon gwamnan ya ce abin kunya ne ace dan yankin kudu, irinsu gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi shine zai zo yayi sulhu tsakanin gwamnan Kano da Sarkin Kano.

A cewar tsohon gwamnan: "Ina su Sarkin Musulmi, Shehun Borno da Sarkin Zazzau? Wannan wani ginshikine aka taba, wanda ya shafi duka wadannan mutanen, muna da manyan malamai, kuma haqqinsu ne su zo su sasanta wadannan mutane guda biyu."

Bafarawa ya ce kamata yayi manyan arewa su hada kwamiti wacce za ta kunshi dattijan arewa, sarakuna, malamai da 'yan kasuwa.

"Shi kansa uban tafiyar, babanmu shugaban kasa Muhammadu Buhari bai dace ace ya zura ido yana kallon wannan abu a yankin shi ba," a cewar tsohon gwamnan.

Bafarawa ya ce yanzu idan Buhari ya kira su ya tsawatar da su shikenan magana ta mutu ba za ta kara tashi ba, saboda shine ubanmu, kuma shugaba a gare mu.

Da aka tambayi tsohon gwamnan, wanda a lokacinsa ne aka nada Sarkin Musulmi Sa'ad na III, a ganinsa menene yake kawo wannan rikici? Sai ya bada amsa da cewa shaidan ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng