Akalla 20% na Malaman Makaranatar Bauchi na bogi ne – Bala Mohammed
Mun samu labari daga Daily Trust cewa sabon gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya bayyana cewa akalla ba a kasara ba, 20% na Malaman makaranta da ake da su a Bauchi na bogi ne.
Gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da ya gana da wasu Matasa a Ranar aka shirya wani biki domin tunawa da Yaran Afrika. Gwamna Mohammed ya ce gwamnatin baya ta yi wannan aiki.
Sanata Bala Mohammed ya koka da cewa an dauki ma’aikata na bogi a jihar Bauchi, a daidai lokacin da ake da kwararrun Malamai wanda ba su da aiki a jihar, don haka ne ya ce zai yi bincike.
Gwamna Bala Mohammed ya sha alwashin bin diddikin abin da gwamnatin baya ta yi domin bankado wadannan Malamai na bogi, tare da kuma binciken kwangilolin da gwamnatin APC ta bada.
KU KARANTA: Kare jinin al'umma ne aikin farko a gaban ka – Moghalu da Buhari
Jaridar ta rahoto gwamnan ya na cewa zai sa kafar wando daya da wadanda su ka hana Bauchi cigaba. Mohammed ya ce zai casa manyan da aka samu da laifin facaka da kudin al’umma a hukumar SUBEB
Bala ya ce: “Na gaza gane abin da gwamnatin da ta shude ta rika yi har ta kyale harkar ilmi ya tabarbare ainun.”
Gwamnan cigaba da cewa:
“A mafi yawan Makarantun Firamare, za ka ga yara su na zama a kasa, ko kuma karkashin bishiya, sannan babu ko rufi a dakunan karatu, duk da irin kudin da ake narkawa hukumar SUBEB”
“Za mu dauki Malaman makaranta mata 1, 000 da kungiyar UNICEF na Duniya da wasu manyan kungiyoyi su ka ba horo kwanakin baya.” Gwamnan ya yi wannan alkawari duk a ranar.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng