Masarautar Rano: Hakimai 4 sun yi kunnen uwar shegu da umarnin da Sarki ya basu

Masarautar Rano: Hakimai 4 sun yi kunnen uwar shegu da umarnin da Sarki ya basu

- An bukaci wasu Hakimai hudu na masarautar Rano da su bayyana kansu a gaban fada, saboda sun ki bin wani umarni da Sarkin Rano ya bayar

- Sarkin ya bukaci Hakiman su bayyana a fadarsa domin shan ruwan azumi, suka yi biris dashi babu wanda ya leka fadar

- Haka kuma Sarkin ya Hakiman su fito domin gabatar da hawan sallah karama tare dashi, nan ma suka yi kunnen uwar shegu dashi

Sabuwar masarautar Rano dake jihar Kano ta fara bincikar Hakimai guda hudu da suka ki bin umarninta.

Hakiman sun hada dana karamar hukumar Doguwa, Alhaji Aliyu Harazimi; karamar hukumar Kura, Alhaji Bello Ado Bayero; karamar hukumar Garun Malam, Alhaji Abubakar Gwadabe Buhari da kuma karamar hukumar Takai, Alhaji Lamido Danburan Haruna.

An fara binciken ranar 17 ga watan Yuni, wanda sakataren masarautar, Muhammad Idris Rano ya sanya hannu akan takardar binciken.

KU KARANTA: Tsugune bata kare ba a Kano: Hukumar yaki da cin hanci ta bukaci a tsige Sarki Sanusi don taji dadin gabatar da bincike akan shi

A cikin takardar an bayyana cewa an aikawa Hakiman hudu da takardar gayyata a cikin watan Azumi, inda aka bukaci su bayyana kansu a fadar Sarkin Rano domin yin bude baki da Sarkin, sannan kuma an bukaci su shirya fitowa hawan sallah tare da Sarkin wanda za ayi a fadarsa.

An kuma bukaci Hakiman da su mayar da martani cikin awa 24, da dalilin da yasa baza a dauki kwakkwaran mataki a kansu ba.

Tun bayan raba masarautar Kano gida biyar ake ta faman samun tashin-tashina da sababbin Sarakunan da aka nada, wanda suka hada da Sarkin Rano, Karaye, Gaya da kuma Sarkin Bichi.

Idan ba a manta ba kwanakin baya Sarkin na Rano ya dakatar da wasu Hakimai guda biyu saboda sun ki bin wani umarni da ya bayar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng