Jam'iyyun PDP, PRP, NNPP su na harin wasu kujerun APC a Jihar Bauchi

Jam'iyyun PDP, PRP, NNPP su na harin wasu kujerun APC a Jihar Bauchi

‘Yan takara 5 na jam’iyyun adawa a jihar Bauchi wanda su ka samu nasara a gaban kotu bayan kammala zaben 2019 sun ga abin mamaki bayan da aka rantsar da ‘yan takarar APC a matsayin ‘yan majalisar tarayya.

Idan ba ku manta ba, a cikin tsakiyar Watan Mayu ne wani kotu da ke Abuja ya umarci INEC ta mikawa wasu ‘yan takarar da su ka zo na biyu a zaben ‘yan majalisar wakilai da dattawa na jihar Bauchi shaidar lashe zabe.

Kujerun da kotu ta taba sun hada da na Sanatan Bauchi ta Kudu da kuma ‘Yan majalisar yankin Zaki, Alkaleri/Kirfi, Darazo/Ganjuwa da kuma Gamawa. Da farko dai jam’iyyar APC ce ta lashe duka wadannan kujeru.

KU KARANTA: Watakila sunayen Ministociya shiga hannun Majalisa a Watan gobe

Kotu ta nemi a ba Garba Dahiru kujerar Sanatan Kudancin Bauchi na jam’iyyar PDP, sannan kuma a mikawa Abdulkadir Ibrahim, da Awwal Jatau takardar shaidar lashe zaben majalisa da ya gabata a jam’iyyar PDP.

Wannan kotu ta kuma nemi INEC ta ba Dayyabu Chiroma, da Isa Mohammed Wabu takardar da ke nuna cewa su ne su ka lashe zaben Mazabun Darazo da Ganjuwa da kuma yankin Gamawa a jam’iyyar PRP da NNPP.

‘Yan takarar jam’iyyar APC da kotu ta karbe kujerun na su sun hada da; Sanata Lawan Yahaya Gumau, Musa Pali, Mansur Manu Soro Tata Umar, sai kuma Honarabul Garba Mohammed Gololo

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng