Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar da Sallar juma'a a masallacin ASD

Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar da Sallar juma'a a masallacin ASD

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana dalilin ta na kafe wa a a kan cewar sai dai a cigaba da sallar Khamsal Salawat a sabon Masallacin da ASD ya gina.

Gwamnatin ta ce ba za a cigaba da sallar Juma'a a Masallacin da ASD ya gina a Yakubu Avenue ba saboda an gina shi ba bisa ka'ida ba.

A cewar gwamnatin, ginin Masallacin ya saba da doka da tsarin ma'aikatar kasa da safayo ta jihar Kaduna.

"Ba haka suka bamu a rubuce ba, sun nemi izinin gina Masallacin Sallah biyar na kowacce rana ne ba ginin babban masallacin juma'a ba, irin Masallacin a nan ne da e gina wa a jikin gida.

"Hukumar tsare-tsare ta jihar Kaduna (KASUPDA) ta sha yi musu tuni a kan cewar ginin Masallacin da suke yi ya saba da irin wanda suka nemi izinin gina wa da farko. Duk da an sanar da su cewa wurin bai dace da ginin Masallacin Juma'a ba amma suka yi kunnen uwar shegu da duk wani kashedi da tuni da gwamnati tayi musu," a cewar gwamnatin jihar Kaduna.

An bude Masallacin ne makonni biyu da suka wuce inda aka gudanar da Sallar juma'a ta farko a cikinsa. Amma bayan sati ya zagayo sai hukuma ta hana gabatar da Sallar Juma'a a Masallacin saboda kin yin biyayya da gangan da masu ruwa da tsaki a ginin Masallacin suka yi.

Duk da ba a hana kowa zuwa Masallacin ba, yanzu haka an saka makulli an garkame shi.

DUBA WANNAN: Wani matashi ya mutu bayan ya saci wani gunki da 'yan kabilar Tiv ke bauta wa a Wukari

Wakilin jaridar Premium Times da ya ziyarci Masallacin ya ce duk da kasancewar akwai jami'an 'yan sanda a wurin, basu hana kowa ya halarci Masallacin ba. Duk wanda ya bi ta wurin da aka gina Masallacin zai gan shi garkame a kulle da makulli.

Tuni jama'a suka kaurace wa Masallacin biyo bayan rufe shi da hukumar ta yi.

Wasu daga cikin mazauna unguwar da wakilin jaridar ya tattauna da su sun bayyana cewar idan za a yi adalci tare da tsage gaskiya, wurin bai dace da a gina Masallacin Juma'a ba saboda cikin unguwa ne da babu wurin da za a ce Sallar juma'a ake gudanar wa.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta umarci masu Masallacin da su gaggauta mayar da shi na yin Salloli biyar kamar yadda suka sanar da gwamnati a takardar neman izinin fara gina shi kuma aka amince nusu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel