Yadda za a magance talauci a Najeriya - Elumelu
Shugaban babban bankin nan na nahiyyar Afirka, United Bank for Africa (UBA), Mista Tony Elumelu, ya shawarci gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda za a magance talauci a kasar nan.
Fitaccen attijirin wanda ya kasance mamallakin gidanauniyar nan ta Elumelu Foundation, ya shawarci gwamnati akan bayar da tallafi wajen inganta jin dadin kananan 'yan kasuwa da kuma kananan masana'antu domin yaye katutu na talauci a tsakanin al'ummar kasar nan.
Mista Elumelu kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito ya bayyana cewa, wannan ita kadai ce mafificiyar hanya da za ta tabbatar da akidar 'Next Level' da gwamnatin shugaba Buhari ta kudirta a wa'adin ta na biyu domin tsamo miliyoyin al'ummar kasar nan daga kangin talauci cikin tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Babban jagoran bankin na UBA ya bayyana wannan shawarwari yayin gabatar da jawaban sa a taron biki yaye dalibai karo na 35 da aka gudanar a jami'ar Bayero dake birnin Kanon Dabo, inda ya samu babban karamci daga jami'ar na daya daga cikin wadanda suka ciri tutu ta bunkasa harkokin kasuwanci a nahiyyar Afirka.
KARANTA KUMA: Buratai zai gabatar da jawabai a taron yaki da ta'addanci na duniya a Landan
Elumelu bai gushe ba yana ci gaba da kyautata zato gami da sa rai a kan gwamnatin shugaban kasa Buhari wajen bunkasar ci gaba a kasar nan tare da tsamo ta daga dukkanin wan kalubale da tale fuskanta domin fidda ita zuwa tudun tsira.
Yayin ci gaba da bayar da shawarwari, Mista Elumelu ya kuma nemi gwamnatin Tarayya da saukaka tsadar haraji a kan kananan 'yan kasuwa tare da saukaka masu harkokin su na gudanar wa wajen bayar da tallafi da kuma kara masu karfin gwiwa.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng