An yi jana'izar marigayi Sanata Babayo Garba Gamawa a mahaifarsa

An yi jana'izar marigayi Sanata Babayo Garba Gamawa a mahaifarsa

A yau Asabar 15 ga watan Yuni ne a kayi jana'izar tsohon mataimakin shuganan jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) na kasa shiyyar arewa, Sanata Babayo Garba Gamawa a mahaifarsa da ke jihar Bauchi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ta ruwaito cewa Sheikh Salisu Ningi ne ya jagoranci sallar da aka yi wa marigayin misalin karfe 11 na safe.

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed yana daya daga cikin manyan mutanen da suka hallarci jana'izar.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 5 da ake gane takardan naira ta jabu

A jawabin da ya yi bayan kammala jana'izar, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai saukin kai tare da jajircewa wurin aiki kuma ya bayar da gudunmawa mai yawa wurin cigaban jihar.

Ya yi addu'ar Ubangiji Allah ya gafarta wa mammacin kana ya bawa iyalansa hakurin jure rashin sa.

Sanata Gamawa ya rasu ne a daren jiya Juma'a a Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Ya rasu yana da shekaru 53 a duniya kuma ya bar matan aure hudu da 'ya'ya 16 tare da mahaifiyarsa da sauran 'yan uwa.

Kafin rasuwarsa, Sanata Gamawa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC bayan an dakatar da shi daga jam'iyyar PDP.

Ya kuma taba rike mukamin mataimakin gwamnan jihar Bauchi a zamanin mulkin gwamna Isa Yuguda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel