Wa'iyazubillah: An kama malamin jami'a tsirara yana kokarin yin zina da dalibarshi

Wa'iyazubillah: An kama malamin jami'a tsirara yana kokarin yin zina da dalibarshi

- Asirin wani malamin jami'a ya tonu inda aka kama shi yana kokarin yin zina da wata dalibarshi

- An kama malamin tsirara haihuwar uwarshi a cikin gidanshi

- An ce malamin yayi kaurin suna wurin amfani da dalibanshi mata kafin ya basu maki

A jiya Juma'a ne aka kama wani malamin jami'a dake koyarwa a bangaren aikin banki a jami'ar jihar Ekiti, dake Ado Ekiti, Dr. O.O Aduwo, tsirara haihuwar uwarshi yana kokarin yin zina da wata dalibarshi wacce aka bayyana sunanta da Nike, wacce ya gayyaceta zuwa gidansa a jiyan.

A cewar wani rahoto da daliban jami'ar suka fitar, Dr Aduwo yayi kaurin suna wajen tilasta dalibansa mata domin suyi zina dashi.

KU KARANTA: Tirkashi: Na yiwa mahaifiyata fyade ne saboda na kasa boye sha'awata - Wani dan shekara 40 ya koka

Jiya Nike da ita da saurayinta da kuma wasu abokananta suka hada baki akan taje gayyatar da malamin yake yi mata, kamar yadda ya nema, A lokacin da take cikin gida, saurayin Nike da kawayenta wadanda suka boye a kofar gidan malamin, sai suka shiga cikin gidan suka kama shi tsirara haihuwar uwarsa yana neman kwanciya da ita.

A wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumunta, malamin ya tsorata sosai bayan an kama shi, an jiyo shi a cikin bidiyon yana rokar daliban da suka kama shi da su rufa masa asiri.

A cewar daliban makarantar, Nike ce ta sanya bidiyon a shafinta na WhatsApp.

Kwanakin baya ma an taba kama wani malamin jami'a wanda ya nemi dalibarsa da ta kwanta dashi kafin ta samu ta ya tsallakar da ita jarrabawa.

Allah ya kyauta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel