Farashin Shinkafa Ya Tashi, Buhu 1 Ya Kama Hanyar N100,000 a Wasu Kasuwannin Najeriya
- Farashin buhun shinkafa 'yar kasae waje mai nauyin kilo 50 ya kai N90,000 a wasu kasuwannin birnin tarayya Abuja
- Bincike ya nuna cewa matsakaicin farashin buhun shinkafa a kasuwanni 37 ya kai N79,207 zuwa ranar 9 ga Nuwamba, 2026
- Masu sayar da shinkafa sun nuna fargabar cewa karin farashin shinkafar waje zai iya shafar ta cikin gida gabanin bukukuwan karshen shekara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Farashin shinkafa ya karu a manyan kasuwannin Najeriya, inda ake sayar da buhun 'yar kasar waje mai nauyin kilo 50 kan kudi har N90,000 a Abuja.
Wannan karin farashi ya janyo damuwa kan yiwuwar sake tashin farashin kayan abinci yayin da ake tunkarar lokacin bukukuwan karshen shekara.

Source: Getty Images
Buhun shinkafar waje ya tashi
Wani binciken kasuwa da Daily Trust ta ruwaito ya nuna cewa farashin wasu nau’ikan shinkafar waje a Abuja ya tashi daga N68,000 zuwa N90,000 cikin mako guda.
A jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya farashin ya ci gaba da kasancewa a wani mataki mai tsada.
Karin farashin ya kuma haifar da fargabar cewa shinkafar da ake nomawa a cikin gida za ta iya yin tsada, saboda yadda nau’ikan shinkafar biyu ke gogayya wajen neman masu saye a kasuwa.
Farashin shinkafa a wasu kasuwanni
Wani rahoton farashin kayayyaki da kamfanin Useagrios ya fitar ya nuna cewa matsakaicin farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 a kasuwanni 37 na fadin Najeriya ya kai N79,207 zuwa ranar 9 ga Nuwamba, 2026.
A Legas, farashin ya kai N85,744 a Kasuwar Mile 12, yayin da Kasuwar Garki Model da ke Abuja ta kai N84,443.
Sauran kasuwannin da aka samu farashi mai tsada sun hada da Kasuwar Oil Mill da ke Jihar Rivers, inda buhun ya kai N83,530; Kasuwar Ogbeogonogo a Jihar Delta, N82,835; da Kasuwar Swali a Jihar Bayelsa, N82,797.

Kara karanta wannan
Sheikh Murtala Asada ya yi zazzafar magana kan tallafin N50,000 da aka fara turawa yan Najeriya
Sai dai Kasuwar Kaduna Central na cikin wuraren da aka samu farashi mafi sauki, inda ake sayar da buhun a kan N74,600.
Shinkafar waje ta kara tsada a Abuja
A wani binciken kasuwa daban da aka gudanar a Abuja, an gano karin farashi mai yawa a shinkafar waje, inda wasu ’yan kasuwa suka ce buhun da a baya suke saya a kan N68,000 yanzu ya koma N90,000.
Wani mai sayar da kayan masarufi a Lugbe ya shaida cewa ya yi mamakin karin farashin lokacin da ya je kasuwa domin sayen kaya a ranar Alhamis din da ta gabata.
Ya bayyana cewa tun farko ana sayar da buhun shinkafar a kan N65,000, daga bisani ya koma N68,000, amma cikin mako guda farashin ya tashi zuwa N90,000.
“Na kasa saye saboda ya wuce kasafin da na yi, don haka sai da na sayi wata ta daban a kan N80,000. Wannan shinkafa ce wadda a baya ban taba saya ba, amma karin farashin ya sa na saye ta a lokacin,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Matashin da ya auri mata 2 rana 1 ya rasu a wani yanayi mai cike da al'ajabi

Source: Facebook
Duk da haka, ya ce shinkafar da ake nomawa a cikin gida ba ta samu irin wannan karin farashi ba tukuna, inda ake sayar da mafi yawancinta tsakanin N63,000 da N65,000 kan buhu mai nauyin kilo 50.
Ya bayyana fargabar cewa farashin shinkafar cikin gida ma zai iya tashi idan farashin shinkafar waje ya ci gaba da karuwa, saboda yadda kayayyakin biyu ke gogayya a kasuwa.
Yadda manoma suka fara gudun shinkafa
Kun ji cewa manoman shinkafa dubu uku da dari biyar na shirin barin aikin noma bayan tafka asarar Naira biliyan 93 sakamakon shigo da shinkafar waje.
Wannan bayani ya fito ne daga wani binciken jin ra'ayin manoma na lokacin rani, inda aka tantance manoma 33,507 a jihohi 13 a matakin gwaji.
Asali: Legit.ng
