'Ba Zaben 2027 Matukar aka Hana Atiku Takara,' Dino Melaye Ya Yi Gargadi

'Ba Zaben 2027 Matukar aka Hana Atiku Takara,' Dino Melaye Ya Yi Gargadi

  • Sanata Dino Melaye ya dauki zafi a wata hira da aka yi da shi game da takarar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na shekarar 2027
  • Melaye ya bayyana cewa za su yi duk abin da ya dace domin ganin sunan Atiku Abubakar ya fito cikin 'yan takarar shugaban kasa
  • Hakan na zuwa ne bayan kotu ta rusa shugabancin ADC da David Mark ke jagoranta da rusa matakan da ya dauka ciki har da takarar Atiku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa babu gudu ba ja da baya kan cewa sai an tabbatar da takarar Atiku Abubakar.

A makon da ya wuce ne a wata kotu ta rusa takarar Atiku Abubakar bayan rusa shugabancin jam'iyyar ADC karkashin David Mark.

Kara karanta wannan

Abokin takaran Atiku ya bayyana dalilin rabuwa da shi ya kama layin Tinubu a APC

Dino Melaye a wajen taro
Jigon ADC, Sanata Dino Melaye. Hoto: Dino Melaye
Source: Facebook

Dino Melaye ya bayyana matakan da za su dauka a wata hira da DCL Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Talata.

Magana kan hukuncin kotu

Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa lokacin Atiku Abubakar ya yi a 2027, inda ya ce babu abin da zai hana Wazirin Adamawa takara a 2027.

Dino Melaye ya ce hukuncin da kotu ta yi na hana Atiku takara ba a yi shi bisa hujja ba, kuma alamu sun nuna cewa siyas aya shiga lamarin.

A bayanin da ya yi, Melaye ya bayyana cewa kotun Allah ya isa ta kasa ta riga ta yanke hukunci kan cewa David Mark ne halastaccen shugaban ADC.

Ya ce:

'Ya za a yi bayan kotun ta yi hukunci a ce wata karamar kotu ta zo ta juya wannan hukunci?'

Melaye ya kara da cewa hukuncin da aka yi ya nuna cewa babu wani kuskure a matakan da aka dauka wajen nada shugabannin ADC.

Kara karanta wannan

Atiku: Dino Melaye ya bada labarin yadda kotu ta kira lauyoyin ADC karfe 11:00 na dare

Melaye ya ce Atiku na nan daram

A bayanan da ya yi, Dino Melaye ya bayyana cewa ya kamata kowane dan ADC ya kwantar da hankalin shi game da abubuwan da suke faruwa.

Ya bayyana cewa ba za su yarda da hana Atiku Abubakar takara ba, domin matukar babu Atiku babu batun zaben shugaban kasar 2027.

'Atiku zai yi takara, Atiku zai yi zabe,'
'Ba inda Atiku zai je, wannan lokacin shi ne. Maganar Atiku ba zai shiga zabe ba, babu ita. Wannan karon ba inda za mu je."
Atiku Abubakar da su Abba Hikima
Atiku Abubakar da 'yan Tinubu Must Go. Hoto: Abba Hikima
Source: Facebook

Ya ce idan Atiku ya ci shugaban kasa zaimaido tallafin man fetur domin saukaka rayuwar 'yan kasa da APC ta jefa su a cikin matsala.

Dino Melaye ya kara da cewa Atiku zai bude iyakokin Najeriya idan ya ci zabe, kuma zai inganta rayuwar matasa da mata a Najeriya.

ADC ta soki APC

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta ƙalubalanci APC mai mulki da ta fuskanci 'yan adawa a akwatin zaɓen 2027 maimakon yin amfani da kotu wajen murƙushe su.

Kara karanta wannan

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da hukuncin kotu kan Atiku da ADC

Darakta janar na yaƙin neman zaɓen ADC, Sanata Austin Akobundu, ya bayyana cewa irin karsashin da mutane suka nuna wa Atiku Abubakar a Sokoto ya firgita APC.

Haka zalika jam'iyyar adawa ta ADC ta zargi gwamnatin tarayya da ƙoƙarin hana 'yan adawa damar shiga zaɓe cikin 'yanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng