Mutane 7 da su kayi bakin jini saboda gwagwarmayar 'June 12'

Mutane 7 da su kayi bakin jini saboda gwagwarmayar 'June 12'

A yau Laraba 12 ga watan Yuni ne 'yan Najeriya ke bukin tunawa da zabe mafi karbuwa ga al'umma a tarihin Najeriya.

Tsohon shugaban mulkin soji, Ibrahim Babangida ne ya soke zaben na ranar 12 ga watan Yunin 1993 wanda marigayi Cif MKO Abiola na tsohuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ya ke kan gaba.

An yi zanga-zanga a sassan Najeriya bayan soke zaben da ya kusa haifar da yakin basasa hakan ya tilastawa tsohon shugaban sojin sauka daga mulki a ranar 26 ga Augustan 2003.

Bayan saukarsa an kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Cif Earnest Shonekan wanda daga bisani Janar Sani Abacha ya hambarar da shi a juyin mulkin da ya yi a ranar 17 ga watan Nuwamban 2003.

Janar Abacha ya mutu a ranar 8 ga watan Yunin 1998.

Yayin da ake ganin akwai 'yan Najeriya da dama da su kayi gwagwarmayar kan zaben na ranar 12 ga watan Yuni, akwai wasu da ake ganin rawar da suka taka na ganin zaben ba tayi tasiri ba ya sa ana musu kallon makiya demokradiyya.

DUBA WANNAN: An gano yadda aka bawa 'yan majalisa toshiyar baki don zaben Gbajabiamila

Ga wasu daga cikin wadanda mafi yawancin mutane da yi wa kallon wadanda suka kawo cikas ga gwagwarmayar ranar 12 ga watan Yuni.

1 - Ibrahim Babangida

Babangida ne shugaban Najeriya a kuma shine ya soke zaben na June 12 da a kayi ittifakin ita ce zabi mafi tsafta a Najeriya. Zanga-zangan da mutane su kayi bayan soke zaben ya tilasta masa sauka daga m22ulki.

2 - Sani Abacha

Tsohon shugaban mulkin sojin na Najeriya yana daga cikin mambobin kwamitin mulkin soji (AFRC) da suka soke zabe.

An yi ikirarin cewa ya taka muhimmiyar rawa wurin soke zaben kuma daga bisani ya rufe wanda ake ganin ya lashe zaben a kurkuku.

3 - Arthur Nzeribe

Tsohon sanatan ya taka muhimmiyar rawa wurin soke zaben mai dimbin tarihi. Shi tare da Abimbola Davies suka kafa 'Association for Better Nigeria' ABN da ta nemi kotu da dakatar da zaben wanda hakan ya bawa gwamnatin Babangida damar soke zaben.

4 - Uche Chukwumerije

Chukwumerije wanda sanata ne a yanzu yana daya daga cikin na hannun daman Abacha da suke rika goyon bayan rashin yin zaben a Najeriya da kasar waje.

5 - Walter Ofonagoro

Shima yana daya daga cikin wadanda suka rika adawa da masu gwagwarmayar ranar 12 ga watan Yuni. Mutane suna yi masa lakabi da kakakin gwamnatin Abacha saboda yadda ya ke kare kudirorin gwamnatin.

6 - Lamidi Adedibu

Tsohon jigon siyasa a Ibadan yana daya daga cikin wadanda su kayi kaurin suna don adawa da gwagwarmayar June 12. Ya dade yana amfana daga gwamnatin soji kuma yana bawa gwamnatin bayanai kan ayyukan kungiyar 'National Democratic Coalition' da ke gwagwarmaya kan June 12.

7 - Abdulazeez Arisekola-Alao

Dan kasuwan mazaunin Ibadan ba zai taba manta abinda ya faru da shi a Jami'ar Ibadan ba a Nuwamban 1998. Ya tafi jami'ar tare da tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar don hallarton yayen dalibai amma daliban suka far masa suka kwace motocin sa suka kona su, da kyar aka tsere da shi cikin motan 'yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel