Jerin Shugabannin Majalisar Dattawan Najeriya da aka yi a tarihi

Jerin Shugabannin Majalisar Dattawan Najeriya da aka yi a tarihi

A daidai ranar da aka nada sababbin shugaban majalisar tarayyar kasar nan. Legit.ng Hausa ta kawo maku jerin sunayen shugaban majalisar dattawan da aka taba yi a tarihin siyasar Najeriya.

Sanata Evan Enwerem da Sanata Chuba Okadigbo su na cikin wadanda aka tsige daga kan wannan kujera. Sanata David Mark ya shafe shekaru 8 yana rike da wannan kujera a jam’iyyar PDP.

Irin su Chuba Okadigbo da Bukola Saraki, duk sun sauya-sheka daga baya zuwa manyan jam’iyyun hamayya. An yi yunkurin sauke Saraki a lokacin yana rike da kujerar amma hakan bai yiwu ba.

Ga dai sunayensu nan da kuma shekarar da su ka rike wannan mukami da kuma jam’iyyar da su ke kai a lokacin da su ka dare kan wannan babbar kujera. Sanata Ahmad Lawan shi ne na 12 a jeringiyar.

KU KARANTA: An bayyana wadanda ya lashe zaben majalisar wakilai

1. Nnamdi Azikiwe shekarar 1960 Jam’iyyar NCNC

2. Nwafor Orizu shekarar 1960-1966 Jam’iyyar NCNC

3. Joseph Wayas shekarar 1979-1983 Jam’iyyar NPN

4. Iyorchia Ayu shekarar 1992-1993 Jam’iyyar SDP

5. Ameh Ebute shekarar 1993 Jam’iyyar PDP

6. Evan Enwerem shekarar 1999 Jam’iyyar PDP

7. Chuba Okadigbo shekarar 1999-2000 Jam’iyyar PDP

8. Anyim Pius Anyim shekarar 2000-2003 Jam’iyyar PDP

9. Adolphus Wabara shekarar 2003-2007 Jam’iyyar PDP

10. David Mark shekarar 2007-2015 Jam’iyyar PDP

11. Bukola Saraki shekarar 2015-2019 Jam’iyyar APC

12. Ahmad Lawan shekarar 2019 Jam’iyyar APC

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel