Abubuwa 5 game da sabon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan

Abubuwa 5 game da sabon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan

A yanzu haka Sanata Ahmed Lawan ne sabon shugaban majalisar dattawa na tara a tarihin dimokuradiyyar Najeriya.

Sanata Lawan ya lashe zaben shugaban majalisar dattawa da aka gudanar a ranar Talata 11, ga watan Yunin 2019 cikin zauren majalisar dake garin Abuja.

Sanata Lawan wanda ya samu kuri'u 79 ya karbi rantsuwa ta kasancewar sa sabon shugaban majalisar dattawan kasar nan bayan ya lallasa Sanata Muhammad Ali Ndume wanda ya samu kuri'u 28 kacal.

Bayan shafe tsawon watanni na tuntube tuntube da neman goyan baya, burin Sanata Ahmed mai wakilcin shiyyar Yobe ta Arewa ya cika yayin da ya kasance shugaban majalisar dattawa yayin da aka kaddamar da sabuwar majalisar Tarayya ta tara a tarihin kasar nan.

Ga wasu muhimman ababe da babu lallai ku na da masaniyar su game da sabon shugaban majalisar dattawan kasar nan.

1. Yayin da yake da shekaru 56 a duniya, an haifi Sanata Ahmed Lawan a shekarar 1959. Ya yi karatun digiri na farko a fannin nazarin albarkatun kasa da sauyin yanayi watau Geography a jami'ar Maiduguri. Ya yi karatun difloma (Postgraduate Diploma), digiri na biyu da kuma na uku a jami'ar Cranfield a kasar Birtaniya. Ya yi bautar kasa a jihar Benuwai.

2. Gabanin kasancewar sa Sanatan shiyyar Yobe ta Arewa, Sanata Lawan bai taba wani aiki ba face karantar wa. Ya shafe tsawon lokuta tun daga mataki na farko yana koyar wa a jami'ar Maiduguri har zuwa lokacin da ya yi ritaya inda ya afka siyasa gadan gadan.

3. Sanata Lawan ya kasance a zauren majalisar Tarayyar kasar nan tun a shekarar 1999 yayin da da aka zabe shi a matsayin mamba na majalisar wakilai. Bayan shafe tsawon shekaru takwas a majalisar wakilai, Sanata Lawan ya samu shiga a majalisar dattawan kasar nan a shekarar 2007 da a halin yanzu ya kasance Sanata mafi samun kwarewa na jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Kai tsaye: Yadda zaben majalisar dokokin tarayya ke gudana

4. Kamar yadda Hausawa kan ce a dade ana yi sai gaskiya, kwarewa gami da kwazon Sanata Lawan sun taka rawar gani inda ya samu kyaututtuka daban daban gami da lambar yabo da dama da suka hadar da martabar CON (National Honours Award of the Commander of the Order of the Niger).

5. Ana kishin-kishin cewa Sanata Lawan na da alaka ta jini da shugaban kasa Muhammadu Buhari. An gano hakan ne yayin da ya yi tattaki da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, yayin wata ziyara da ta kai birnin Jos domin yiwa tsohon Gwamna Tanko Al-Makura ta'aziyya ta rasuwar mahaifiyar sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel