Kaji tsoron Allah kayi adalci a cikin al'umma - Onitiri ya shawarci shugaba Buhari

Kaji tsoron Allah kayi adalci a cikin al'umma - Onitiri ya shawarci shugaba Buhari

- An shawarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi adalci a cikin al'umma a wannan mulkin da zai yi karo na biyu

- Dan takarar Sanata a jam'iyyar PDP ne ya bayar da shawarar

- Ya ce ya zama tilas ya bayar da shawarar ganin yadda matasa ke kashe kansu babu gyara babu dalili a wanna lokacin

An shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari yaji tsoron Allah yayi mulki na adalci a wannan wa'adin nasa na karo na biyu.

Sannan kuma an shawarce shi ya bi dokar kasa, ya kuma bai wa kowanne kabilu hakkinsu, kuma yi adalci wurin bayar da mukaman gwamnati.

Adesunbo Onitiri, dan takarar Sanata a babbar jam'iyyar adawa ta PDP, shine ya bayar da shawarar a lokacin da yake nuna damuwarsa akan matsalar tsaro da kuma tabarbarewar tattalin arziki a kasar nan.

KU KARANTA: Shugaba Buhari: Ni talaka ne kuma masoyana ma talakawa ne

Sannan kuma ya shawarci gwamnatin APC kada ta tafiyar da mulkin kasar nan akan iya tsare-tsaren ta kawai.

Onitiri yace ya zama tilas ya bayar da shawarar ganin yadda yanzu ake ta faman samun matasa na kashe kansu babu gyara babu dalili.

"Kullum kara samun matasa ake yi suna kashe kansu. Tattalin arzikin kasar nan kullum kara lalacewa yake yi.

"Kullum hukumar yaki da cin hanci da rashawa bata da aiki sai bin mutane tana kamawa kuma hakan bai kawo wani canji a kasar nan. Ba haka bane hanyar da ya kamata abi ba domin yakar cin hanci ba a kasar nan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel