Asara uku da goma: Kotu ta sake amshe kujerar majalisar wakilai daga hannun APC ta mika ma PDP

Asara uku da goma: Kotu ta sake amshe kujerar majalisar wakilai daga hannun APC ta mika ma PDP

Wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja, ta soke nasarar da zababben sabon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Zaki ta jahar Bauchi a karkashin jam’iyyar APC, Omar Tata ya samu.

Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia Bello Kawu ne ya yanke wannan hukunci a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu, inda ya bayyana sanar da sunan Tata a matsayin wanda ya lashe zaben a matsayin haramun.

KU KARANTA: Sabon gwamnan Zamfara ya fantsama cikin daji farautar yan bindiga

Asara uku da goma: Kotu ta sake amshe kujerar majalisar wakilai daga hannun APC ta mika ma PDP

Auwal Jatau da Omar Tata
Source: UGC

Don haka Alkalin Bello Kawo ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC data mika ma abokin hamayyarsa na PDP Jatau Muhammad Auwal shaidar samun nasarar lashe zabe, wanda shine yazo na biyu a zaben.

A cewar kotun, jam’iyyar APC bata dan takara, kuma babu yadda za’ayi ta tsayar da dan takara a zaben kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Zaki ta jahar Bauchi a zaben 2019.

Dalili kuwa shine, dan takarar jam’iyyar PDP, Jatau Muhammad Auwal ya shaida ma kotun cewa dan takarar jam’iyyar APC bai cancanci tsayawa takara ba sakamakon jam’iyyar bata gudanar da zaben fidda gwani ba wajen tsayar dashi takara ba.

Don haka Jatau ya kalubalanci nasarar da hukumar INEC tace Tata ya samu a zaben watan Feburairu na 2019, ita kotun ta gamsu da jawaban Jatau, inda ta bayyana kuri’un da Tata ya samu a matsayin haramtattu, don haka ta sokesu duka, da haka Jatau ya zamo sabon dan majalisa.

Wannan hukunci ba shi bane farau ba da kotu take kwace ma jam’iyyar APC mukamanta tana mikasu ga jam’iyyn hamayya, musamman ma jam’iyyar PDP, kuma hakan ya faru ne sakamakon karan tsaye da jam’iyyar APC tayi ma dokokinta da dokokin zabe a wasu jahohin da take da mulki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel