Zanga-zanga: Jami'an tsaro sun shiga farautar mabiya Shi'a a Abuja

Zanga-zanga: Jami'an tsaro sun shiga farautar mabiya Shi'a a Abuja

An shiga dar-dar a babban birnin tarayya Abuja a yayin da jami'an tsaro suka fara farautar 'yan kungiyar Islamic Movement Of Nigeria (IMN) da akafi sani da Shi'a da aka gano suna shirin gudanar da babban zanga-zanga a masallacin kasa da ke Abuja.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa an tsaurara matakan tsaro a waje da cikin birnin Abuja wanda hakan ya janyo cinkoson motocci a Mararaba zuwa Nyanya

Masu ababen hawa da dama sun shiga cikin matsatsi sakamakon shingen da jami'an tsaro suka kafa a mahadar AYA.

DUBA WANNAN: Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba

Cinkoson motoccin da ya fara daga AYA ya kai Masaka zuwa Orange Market wanda hakan ya tilastawa mutane da dama takawa da kafa ko amfani da babur domin su isa wuraren da za su tafi.

Jami'an tsaro sun gano shirin da 'yan kungiyar su kayi na gudanar da zanga-zangar hakan yasa suka dauki matakin gaggawa na ganin ba a samu tabarbarewar tsaro ba.

A ranar Juma'ar makon da ta gabata, 'yan kungiyar sun tare Shugaba Muhammadu Buhari na tsawon wasu sa'o'i yayin da ya tafi yin sallar Juma'a a masallacin kasa da ke Abuja.

Kungiyar na cigaba da zanga-zanga ne saboda cigaba da tsare shugaban su, Ibraheem El-Zakyzaky da aka kama tun 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel