Tsofin gwamoni 4 a mulkin soji sun halarci bikin rantsar da Badaru a jihar Jigawa

Tsofin gwamoni 4 a mulkin soji sun halarci bikin rantsar da Badaru a jihar Jigawa

A yayin da ake rantsar da shugaban kasa da ragowar gwamnoni 29 da aka zaba a fadin kasa, tsofin gwamnonin jihar Jigawa hudu da suka jagoranci jihar a mulkin soji sun halarci bikin sake rantsar da zababben gwamnan jihar, Mohammed Abubakar Badaru, a karo na biyu.

Tsofin gwamonin jihar Jigawa a mulkin soji da suka hada; laftanal kanal Abubakar Sadiq Zakariyya Maimalari (mai ritaya), birgediya janar Olayinka Sule (mai ritaya), birgediya jana Rasheed Shekoni (mai ritaya) da birgediya janar Ibrahim Aliyu (mai ritaya), sun halarci bikin rantsar da Badaru.

Tsofin sojoji hudu ne suka taba rike mukamin gwamnan jihar Jigawa bayan an kirkiri jihar daga tsohuwar jihar Kano a shekarar 1991.

Da yake gabatar da jawabi jim kadan bayan kammala rantsar da shi a filin taron na Aminu Triangle dake Duste, babban birnin jihar Jigawa, gwamna Badaru ya bayyana cewar tun bayan hawansa mulki yake ware kaso biyar 5% na kasafin kudin jihar domin aiyukan inganta lafiyar jama'a, ya bayyana cewar ya kashe biliyan N11.5 a bangaren lafiya a zangonsa na farko.

Tsofin gwamoni 4 a mulkin soji sun halarci bikin rantsar da Badaru a jihar Jigawa
Taron rantsar da gwamnan jihar Jigawa
Asali: Facebook

Tsofin gwamoni 4 a mulkin soji sun halarci bikin rantsar da Badaru a jihar Jigawa
Badaru yayin gabatar da jawabi bayan an rantsar da shi
Asali: Facebook

Tsofin gwamoni 4 a mulkin soji sun halarci bikin rantsar da Badaru a jihar Jigawa
Badaru na karbar rantsuwa daga alkalin alkalan jihar Jigawa
Asali: Facebook

A cewar sa, ya gina dakunan karbar magani 82, manyan asibitoci guda hudu da asibitin kawarru guda biyu, wadanda ya ce ana kan aikinsu.

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta kashe biliyan N15.7 domin samar da ruwa ta hanyar gina gidajen ruwa masu amfani da hasken rana, ya ce an kuma inganta tsofin gidajen ruwa a sassan jihar.

DUBA WANNAN: An kunyata Oshiomhole saboda saba ka'ida a wurin rantsar da Buhari

"Gwamnatina tayi nasarar gina cibiyar kula da lafiya a kowacce mazaba. Mun gina cibiyoyin lafiya a mazabu 287 dake jihar Jigawa.

"Mun sada kaso 95% na mutanen jihar Jigawa da ruwan sha mai tsafta, Jigawa ce jiha ta farko a arewa sannan ta hudu a duk Najeriya a sahun jihohin da suka samar da tsaftataccen ruwa domin amfanin jama'a," a cewar gwamna Badaru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel