Ayyuka 25 da shugaba Buhari zai yiwa 'yan Najeriya bayan an rantsar dashi yau

Ayyuka 25 da shugaba Buhari zai yiwa 'yan Najeriya bayan an rantsar dashi yau

- Jerin alkawuran zabe guda 25 da shugaban kasa Muhammadu ya dauka zai yi bayan an rantsar da shi

- Majiyarmu Legit.ng ta yi kokarin kawo muku su daya bayan daya

Yau ce ranar rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari, yanzu haka dai har filin wasa na Eagle Square ya fara canja kala, yayin da za a rantsar da shugaban kasar a karo na biyu.

Ana sa ran abubuwa da dama daga gurin shugaban kasar a wannan shekaru hudun da zai yi, kamar yadda ya ce, "wannan shi ne karo na biyar kuma karo na karshe da zai tsaya takara a Najeriya."

Ayyuka 25 da shugaba Buhari zai yiwa 'yan Najeriya bayan an rantsar dashi yau
Ayyuka 25 da shugaba Buhari zai yiwa 'yan Najeriya bayan an rantsar dashi yau
Asali: Facebook

Ga wasu daga cikin alkawuran da shugaban kasar yayi a lokacin yakin neman zabe:

1. Alkawarin kai Najeriya tudun mun tsira wato (NEXT LEVEL).

2. Samawa matasa miliyan 1 da suka kammala digiri aikin N-Power.

3. Koyawa 'yan Najeriya miliyan 10 sana'ar hannu.

4. Bai wa manoma miliyan 1 iri da kayan aikin gona.

5. Kirkirar ayyuka miliyan daya da rabi a bangaren noma da kiwo.

6. Kirkirar ayyuka miliyan 5 a bangaren noma.

7. Samar da dala miliyan 500 don samar da ayyuka 500,000 ga 'yan Najeriya

8. Koyawa matasa 200,000 kasuwanci a fannin fasaha.

9. Gina wuraren shakatawa guda 6 a yankunwa 6 na fadin kasar nan.

10. Kara shirin ciyar da yara dalibai daga miliyan 9 zuwa miliyan 15.

11. Shirin ciyarwa don samar da karin ayyuka 300,000 ga masu karamin jari da manoma.

12. Kammala hanyar jirgin kasa ta Lagos zuwa Calabar, kammala aikin 2nd Niger Bridge, kammala hanyar Abuja zuwaa Kano.

KU KARANTA: Taba kidi taba karatu: Jerin hutun da 'yan Najeriya za su samu a cikin wannan shekarar

13. Kammala aikin titin jirgin kasa na Ibadan zuwa Kano, da kuma Port Harcourt zuwa Maiduguri.

14. Kara karfin kafafe sadarwa zuwa kilomita 120,000 a fadin Najeriya.

15. Kara karfin wutar lantarki zuwa 1000MW kowacce shekara.

16. Kara yawan raba wutar lantarki zuwa 7000MW, kirkirar jami'o'i guda 9, kasuwanni 300.

17. Aiwatar da shirin samar da wutar lantarki a yankunan karkara na dala miliyan 550.

18. Bayar da bashin miliyan 1 ga masu sana'ar hannu.

19. Kara kudin TraderMoni daga miliyan 2 zuwa miliyan 10.

20. Gina shaguna 109 ga hukumomin (CAC, NAFDAC, SON da sauran su).

21. Sake koyar da malaman makarantar firamare dana sakandare.

22. Gyara makarantu 10,000 kowacce shekara.

23. Shigo da tsarin Co-Payments don biyan kudin inshora na fannin lafiya.

24. Cire kashi 40 cikin 100 na marasa hali daga cikin tsarin Co-Payments.

25. Kara yawan mutanen da suke amfani da tsarin kula da kiwon lafiya daga kashi 12 zuwa kashi 45 cikin 100 a shekarar 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel