Abubuwa 5 da za su faru a wannan mako cikin Najeriya da Duniya baki daya

Abubuwa 5 da za su faru a wannan mako cikin Najeriya da Duniya baki daya

A yayin da yau take Litinin manuniya ta shigar mu sabon mako, ko shakka babu akwai wasu muhimman ababe biyar da za su auku a Najeiya da kuma ilahirin duniya baki daki. Faruwar wannan ababe na ci gaba da kan harsunan al'umma.

A yayin da muke fatan samun iko na Ubangiji, ga jerin ababe biyar da muke sa ran faruwar su cikin wannan mako ga wanda Mai Duka ya azurta da tsawon rai.

1. Rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari yayin rantsuwa a wa'adin sa na farko
Shugaba Buhari yayin rantsuwa a wa'adin sa na farko
Asali: UGC

A ranar Laraba, 29 ga watan Mayun 2019, da ta yi daidai da ranar Dimokuradiyya a kasar nan, za a rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a wa'adin sa na biyu na riko da akalar jagorancin kasar Najeriya bayan ya lashe babban zaben kasa da aka gudanar a watan Fabrairun 2019.

2. Rantsar da Gwamnoni wasu jihohin Najeriya

Yayin rantsar da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi
Yayin rantsar da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi
Asali: Depositphotos

Kazalika a ranar Larabar dai ta wannan mako za a rantsar da wasu gwamnonin Najeriya biyo bayan nasarar lashe zaben gwamnoni da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris na 2019.

3. Ranar Kudus

'Yan shi'a a Najeriya
'Yan shi'a a Najeriya
Asali: UGC

A ranar Juma'ar wannan mako da za ta kasance Juma'ar karshe cikin watan Ramadana na bana, ana sa ran mabiya akidar Shi'a za su yi tattaki domin tunawa da ranar Kudus kamar yadda suka saba a kowace shekara.

Mabiya akidar Shi'a sun saba gudanar da wannan tattaki da manufa ta nuna jimami dangane da subucewar masallacin baitul maqdis dake birnin Kudus daga hannun Musulmai zuwa Yahudu.

4. Gasar Kofin Zakarun Turai ta Europa League

Kofin Zakarun Turai na Europa League
Kofin Zakarun Turai na Europa League
Asali: Getty Images

A ranar Laraba ta wannan mako za a yi karon batta tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da kuma Chelsea a filin wasa na Olympic dake birnin Baku na kasar Azerbaijan domin tantance zakarun Turai na gasar Europa League na bana.

5. Gasar Kofin Zakarun Turai ta Champions League

Kofin Zakarun Turai na Champions League
Kofin Zakarun Turai na Champions League
Asali: Getty Images

A ranar Asabar, 1 ga watan Yuni, za a tantance zakarun Turai na gasar Champions League, inda za a fafata tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da kuma Tottenham a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid a kasar Andalus watau Spain.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel