Nagode da baka musuluntar dani ba – Rotimi Amaechi ga Shugaba Buhari

Nagode da baka musuluntar dani ba – Rotimi Amaechi ga Shugaba Buhari

- Ministan sufuri, Rotimi Amaechi yayi godiya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan rashin mayar dashi Musulmi

- Ameachi yace ya sha caccaka lokuta da dama kan cudanya da Shugaban kasar wanda mutane da dama ke zargi da yunkurin Musuluntar da Najeriya

- Tsohon gwamnan na jihar Rivers yace akwai lokacin da aka mayar da sunansa Alhaji Rotimi Chibuike Amaechi saboda kusancinsa da Buhari

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu cikin barkwanci yayi godiya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan rashin mayar dashi Musulmi, cewa ya sha caccaka lokuta da dama kan cudanya da Shugaban kasar wanda mutane da dama ke zargi da yunkurin Musuluntar da Najeriya.

Amaechi ya bayyana hakan ne a taron majalisar zartarwa na karshe wanda ya gudana a fadar Shugaban kasa da ke Abuja a jiya Laraba.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana yadda saura kiris a fatattake shi daga cocin Christ the King Catholic Church a shekarar 2014 saboda goyon bayan Shugaban kasar, wanda suka yi zargin cewa yana kokarin Musuluntar da Najeriya.

Nagode da baka musuluntar dani ba – Rotimi Amaechi ga Shugaba Buhari

Nagode da baka musuluntar dani ba – Rotimi Amaechi ga Shugaba Buhari
Source: UGC

“Ya Shugaban kasa, bari nag ode maka da baka musuluntar dani ba. Na fadi hakan ne musamman saboda a 2014 lokacin da na shiga cocin Christ the King Catholic Church, an kusa yi mani kora da hali a matsayin gwamna saboda an zarge ni da goyon bayan mutumin da ke da akidar musuluntar da Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Muhimman ayyukan ibada 10 da ya kamata mai azumi yayi a goman karshe na Ramadana

“Kuma a jihar Rivers sai aka fara kira na da ‘Alhaji Rotimi Chibuike Amaechi’. Na gode maka saboda sun ajiye ‘Alhajin’sannan sun koma kira da Mista Chibuike Amaechi,’’ inji shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel