A karon farko Sheikh Dahiru Bauchi yayi karin haske akan raba masarautun Kano

A karon farko Sheikh Dahiru Bauchi yayi karin haske akan raba masarautun Kano

Shararren malamin addinin Musuluncin nan, kuma shugaban Darikar Tijjaniyya na Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi karin haske dangane da ra'ayoyinsa kan rarraba masarautar Kano da Ganduje yayi

Ya yi bayanin cewa ko Turawan mulkin mallaka ba su raba masarautar ba kamar yadda gwamnan Kanon ya raba a wannan lokacin ba.

Sannan ya kuma yi bayani dangane da matsalar tsaro da irin halin da al'umma suke ciki a wannan lokacin.

A karon farko Sheikh Dahiru Bauchi yayi karin haske akan raba masarautun Kano
A karon farko Sheikh Dahiru Bauchi yayi karin haske akan raba masarautun Kano
Asali: Facebook

Ga yadda hirar ta kaya tsakaninsa da 'yan jarida:

Me za ka ce game da raabaa masarautar jihar Kano?

Duk abinda ya shafi Kano ya shafi dukkaninmu 'yan Tijjaniyya na Naajeriya. Abinda na cin mutuncin da za ayi wa fadar Kano ko kuma Kano, Turawa sun zo sun ci kasar nan, sun shekara 60 suna shegantakarsu amma ba su taba fadar Kano ba.

Bayan su 'yan siyasa sun gaje su aka samu gwamnonin siyasa wajen guda bakwai a Kano, sannan aka samu gwamnonin mulkin soja wajen guda tara a Kano, duk dai wadannan ba su nemi cin mutunci da kekketa sha'anin fadar Kano ba, sai wannan karon aka samu.

Amma ba don an ce kotu ta riga ta dakatarda maganar ba, da na yi niyyar zan yi jaje ga dukkan 'yan Tijjaniyyar Najeriya akan abinda ya same mu, domin muhimmancin Kano. Saboda haka haduwar Shehu da Kano, haduwar mu da Kano, duk mutanen da yake saduwa da su a Kano, yana daukar su ne kamar mutanen Kano. Hakanne yasa muke damuwa akan matsalar fadar Kano.

KU KARANTA: Kaka kara kasa: Kwana daya bayan kammala rantsar da Buhari, Igbo suma za suyi ta su rantsuwar

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa al'umma za ta amfana da raba masarauta da aka yi. Ka gamsu da wannan bayanin?

Jama'ar Kano sun ce ba sa so. Masarauta sun ce ba sa so. To wa aka yi wa? Idan dai alkairi ne, wa aka yi wa?

Akwai wani karin bayani da za ka yi akan harkar tsaro a Najeriya?

Halin da kasa take ciki ba shi da kyau. Amfanin gwamnati shine ta tsare rayukan mutane kada a hallakar dasu. Ta kuma tsare dukiyoyin mutane kada a salwantar, ta tsare gabobin mutane kada a zubar da jinin su. Sannan kuma ta tsare mutuncinsu, idan gwamnati ta addini ce a tsare masu addininsu.

To amma yanzu duk wadannan abubuwa dana lissafo sun zuba a kasa, ana karkashe mutane babu iyaka, ana kokkona musu dukiyarsu, ana kwakkwashe musu dukiyarsu, babu zaman lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel