Jerin ministocin Buhari, sunaye, ma'aikatu da kuma jihohin su

Jerin ministocin Buhari, sunaye, ma'aikatu da kuma jihohin su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 22 ga watan mayun 2019, ya jagoranci zaman majalisar zantwar na bankwana yayin da rage saura sati daya a rantsar da shi a kan wani sabon wa'adi na jagorancin kasar nan karo na biyu.

A yau ne shugaban kasa Buhari zai karkare zaman majalisar zantarwa na mako-mako da aka ska saba gudanar wa a fadar sa ta Villa da ke garin Abuja.

Jerin ministocin Buhari, sunaye, ma'aikatu da kuma jihohin su

Jerin ministocin Buhari, sunaye, ma'aikatu da kuma jihohin su
Source: Twitter

Majalisar zantarwa ta Najeriya ta kunshi shugaban kasa, mataimakin sa, Ministoci, shugaban ma'aikatan gwamnati na baki daya da kuma shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

KARANTA KUMA: Hukumar jiragen sama ta kasa NCAA ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani

Ana ci gaba da cece-kucen cewa akwai yiwuwar shugaban kasa Buhari zai sallami dukkanin Ministoci bayan kammala zaman majalisar zantarwa na bankwana domin samun damar nadin sabbi da za su rike madafan iko a wa'adin gwamnatin sa na biyu.

Tiryan Tiryan ga jerin Ministocin shugaba Buhari, sunaye, ma'aikatu da kuma jihohin da suka fito a fadin Najeriya kamar haka:

1. Ministan Labarai da Al'adu; Alhaji Lai Muhammad (Jihar Kwara)

2. Ministan Kwadado; Chris Ngige (Anmabra)

3. Ministan Sufuri; Rotimi Amaechi (Ribas)

4. Ministan Makamashi, Ayyuka da Gidaje; Babatunde Fashola (Legas)

5. Ministan harkokin cikin gida; Abdulrahman Dambazau (Kano)

6. Ministan Kimiya da Fasaha; Ogbonaya Onu (Ebonyi)

7. Ministan Shari'a kuma Lauyan Kolu na kasa; Abubakar Malami (Kebbi)

8. Ministan Sufurin jiragen Sama; Hadi Sirika (Katsina)

9. Ministan Sadarwa; Adebayo Shittu (Oyo)

10. Ministan Ruwa; Suleiman Adamu (Jigawa)

11. Ministan Matasa da wasanni; Solomon Dalong (Filato)

12. Ministan Man Fetur; Ibe Kachikwu (Delta)

13. Karanin Ministan Lafiya; Dakta Osagie Ehanire (Edo)

14. Ministan Noma; Audu Ogbeh (Benuwai)

15. Ministan kasafi da tanadin kasa; Udo Udo Udoma (Akwa Ibom)

16. Karamin Ministan Zamantakewa; Ibrahim Usman Jibril (Nasarawa)

17. Ministan Neja Delta; Claudius Omoyele Daramola (Ondo)

18. Ministan Ilimi; Anthony Onwuka (Imo)

19. Ministan harkokin kasashen ketare; Geoffery Onyeama (Enugu)

20. Ministan Tsaro; Masur Dan Ali (Zamfara)

21. Ministan Kudi; Zainba Ahmed (Kaduna)

22. Ministan masana'antu da hannun jari; Okechukwu Enelamah (Abia)

23. Ministan Birnin Tarayya; Muhammad Bello (Adamawa)

24. Ministan Makamashi; Mustapha Baba Shehuri (Borno)

25. Ministan Harkokin Mata; Aisha Abubakar (Sakkwato)

26. Karamin Ministan Noma; Heineken Lokpobiri (Bayelsa)

27. Ministan Ilimi; Adamu Adamu (Bauchi)

28. Ministan Lafiya; Isaac Adewole (Osun)

29. Ministan Neja Delta; Usani Uguru (Kuros Riba)

30. Karamin Ministan Ma'adanan kasa; Abubakar Bawa Bwari (Neja)

31. Ministan Zamantakewa; Suleiman Hassan (Nasarawa)

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel